bbc.co.uk navigation

'Yan gudun hijira daga Mali sun isa Nijar

An sabunta: 20 ga Maris, 2012 - An wallafa a 16:59 GMT

'Yan gudun hijira daga Mali sun isa Nijar

  • 'Yan gudun hijira daga Mali sun isa Nijar
    Kimanin 'yan gudun hijira 6,000 ne suke neman mafaka a kauyen Chinedogar na kan iyakar jamhuriyar Nijar da kasar Mali, bayan da suka tserewa rikicin da ake fama da shi a Malin. Tun ranar 17 ga watan Janairu ne 'yan tawaye ke fada domin samun 'yanci daga hukumomi a Arewacin kasar ta Mali.
  • 'Yan gudun hijira daga Mali sun isa Nijar
    Yawancin 'yan gudun hijirar sun fito ne daga yankin Menaka. Sun iso Nijar ne kodai a kan Jakuna ko kuma a kasa, inda kuma suke zaune a wasu tantuna da aka kafa a wajen kauyen.
  • 'Yan gudun hijira daga Mali sun isa Nijar
    Mata da kananan yara ne dai suka fi shiga cikin kunci, wasunsu sun shafe mako guda anan ba tare da samun abincin da za su kai bakinsu ba.
  • 'Yan gudun hijira daga Mali sun isa Nijar
    Aroureiny Ag Amatou, Magajin garin Adramboucar, sanye da farar babbar riga da bakin rawani ya ce : " 'yan tawaye sun kaiwa sansanin sojoji hari lokacin da suka shiga garin, kuma kowa ya shiga cikin rudani".
  • 'Yan gudun hijira daga Mali sun isa Nijar
    "A yanzu mun kubuta bayan isowarmu nan" a cewar wata mata da ta iso daga Mali tare da 'ya'yanta goma.
  • 'Yan gudun hijira daga Mali sun isa Nijar
    Wani dan gudun hijirar ma ya bayyana yadda harin 'yan tawayen ya kasance. "Yan tawayen sun yi ruwan bama-bamai a kan garin, ciki harda sansanin soji da sauran gine-ginen gwamnati...sannan suka yi watsi da kayayyakin aiki da suka hada da na'urorin kwamfiyuta."
  • 'Yan gudun hijira daga Mali sun isa Nijar
    Har yanzu mutane sun ci gaba da tserewa. Ahamd Issa wani matashi da ya yi gudun hijira zuwa Adramboucar tare da wasu mutane ya ce "'yan tawayen sun nemi jama'a da su zauna, amma mutane sun ci gaba da tserewa."

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.