bbc.co.uk navigation

Hotuna:Yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya

An sabunta: 9 ga Janairu, 2012 - An wallafa a 16:14 GMT

Hotuna: yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya

  • Hotuna: yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya
    Dudun-dubatar mutane suka shiga yajin aiki da zanga-zangar sai baba-ta-gani a Najeriya domin nuna adawarsu da matakin gwamnatin kasar na janye tallafin man fetur.
  • Hotuna: yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya
    Dubban jama'a ne suka taru a Legas da sanyin safiya inda suka rinka kalaman batanci ga shugaba Goodluck Jonathan da kuma gwamnatinsa.
  • Hotuna: yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya
    A jawabinsa ga masu zanga-zangar a Legas, jagoran kungiyar Save Nigeria, kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta CPC a zaben watan Afrilu Mr Tunde Bakare, ya yi jawabi ga masu zanga-zanga a Ojota Legas: "Wajibi ne mutane su tashi tsaye su kwatowa kansu 'yanci".
  • Hotuna: yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya
    Masu zanga-zangar sun kona tayoyi tare da mamaye tituna domin nuna fushinsu
  • Hotuna: yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya
    Rahotanni sun ce 'yan sanda sun kashe mutum guda a Legas, yayin da ka budewa masu zanga-zangar wuta a Kano, bayan da suka yi yunkurin shiga fadar gwamnatin jihar.
  • Hotuna: yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya
    Masu zanga-zangar sun sha alwashin ci gaba da gudanar da ita har sai gwamnati ta sauya matsaya kan batun cire tallafin
  • Hotuna: yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya
    Masu zanga-zanga sun kwanta a kan tituna domin nuna rashin amincewa da matakin gwamnatin Najeriya na janye tallafin mai a Legas.
  • Hotuna: yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya
    Rahotanni sun kuma ce yajin aiki da zanga-zanga sun tsananta a jihohin Nasarawa da Kwara da Benue da kuma Kogi a tsakiyar kasar.
  • Hotuna: yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya
    A jihar Kaduna tsohon gwamnan jihar a lokacin jamhuriya ta biyu Alhaji Balarabe Musa da kuma dan fafutukar kare hakkin bil'adama Shehu Sani, su ne suke jagorantar dubun-dubatar masu zanga-zanga. Yayin da a Kano manyan malaman jami'a suka fito domin baiwa masu zanga-zangar goyon baya. Hoto Nura Muhammad Ringim
  • Hotuna: yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya
    Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun nuna cewa babu banbancin addini a tsakaninsu, a yayin da suka yi Allah wadai da matakin gwamnatin
  • Hotuna: yajin aikin 'yan kwadago a Najeriya
    A jihar Naija ma dubban masu zanga-zanga ne suka fita kan tituna kafin daga bisani su isa Majalisar dokokin kasar. Hoto daga Musa Aliyu jihar Naija

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.