bbc.co.uk navigation

Dubban mutane sun yi zanga-zanga a fadin Najeriya

An sabunta: 3 ga Janairu, 2012 - An wallafa a 18:04 GMT
  • Masu zanga-zanga a Legas
    Daruruwan masu zanga-zanga ne suka mamaye titunan birnin Legas don nuna adawa da janye tallafin man fetur.
  • Masu zanga-zanga a Legas
    Masu zanga-zangar sun rike kwalayen da ke Allah-wadai da gwamnati da ma, kamar yadda kwalin da ake gani a wannan hoton ke nunawa, Shugaba Goodluck Jonathan.
  • Masu zanga-zanga a Legas
    Fitattun mutane da dama ne suka halarci zanga-zangar, ciki har da fitaccen lauyan nan, Femi Falana (na biyu daga dama a wannan hoton)
  • Masu zanga-zanga a Legas
    Masu zanga-zangar sun yi tafiyar fiye da kilomita ashirin a cikin birnin na Legas dauke da kwalaye da ke Allah-wadai da janye tallafin.
  • Masu zanga-zanga a Legas
    Masu zanga-zangar sun yi kira ga 'yan Najeriya su ki amincewa da janye tallafin, su kuma ki amincewa da kara kudin wutar lantarki.
  • Mai sayar da mai a Legas
    Tun bayan sanarwar janye tallafin, farashin mai ya ninka fiye da sau biyu. Masu zanga-zanga a Legas sun yi yunkurin hana gidajen mai sayar da lita guda a kan farashin da ya haura naira sittin da biyar.
  • Masu zanga-zanga a Legas
    Masu zanga-zanga suna cinnawa tayoyi wuta a kan daya daga cikin titunan Legas.
  • Masu zanga-zanga a Legas
    Masu zanga-zanga sun cinnawa tayoyi wuta a kan titunan birnin Legas.
  • Masu zanga-zanga a Legas
    Tayoyin da masu zanga-zangar suka kona a kan tituna sun kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa a titunan birnin Legas.
  • Masu zanga-zanga a Kano
    A birnin Kano ma masu zanga-zanga sun fito don nuna adawa da janye tallafin man.
  • Masu zanga-zanga a Kano
    Daruruwan mutane ne suka fito don gadanar da zanga-zangar nuna adawa da janye tallafin man a birnin Kano.
  • Masu zanga-zanga a Kano
    Masu zanga-zangar a birnin Kano dauke da kwalin da ke bukatar a saki daliban da aka kama.

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.