Hotunan 'yan Najeriya
-
An kaddamar da wani littafi da aka sadaukar domin hotunan Najeriya na zamani da ake dauka. An kaddamar da shi ne a biranen Legas da London. Littafin na kunshe da hotunan da wasu masu kirkirar fasaha tara suka dauka, wadanda suka hadar da George Osodi, wanda shi ne ya dauki wannan hoto da aka sanya wa suna yaron Ogoni. A jerin hotunan da ya dauka a kan yankin Naija Delta mai arzikin man fetur, ya duba illar da kwararar mai ke yi ga 'yan adam da muhalli a yankin.
-
Wannan hoton, wanda shi ma Mr Osodi ne ya dauke shi, na bayyana yadda ake sarrafa rogo, daya daga cikin abincin da 'yan Nayeriya suka fi ci. Jerin hotunan da aka wallafa game da Najeriya dai basu da yawa, domin kuwa guda dubu daya aka wallafa. Ebi Atawodi, shi ne ya tace su, sannan Daraktan kirkire-kirkire na kamfanin zane-zane na Inden da ke Abuja da Legas ya sanya ido a kan yadda aka tsara su.
-
Wannan hoton mai suna 'jiran tsammani' da Emeka Okereke ya dauka shi ne a jikin bangon littafin. Ya dauke shi ne a birnin Paris na kasar Faransa. Birnin Lagos, duk da girmansa, bashi da jiragen kasa masu zairga-zirga a karkashin kasa. Editan littafin hotunan ya ce: "hoton ya bayyana matsayin ci gaban kasarmu a takaice. Ko dai mu yi ayyukan da za su sanya mu ci gaba kamar yadda suka samu, idan ba haka ba, mu ci gaba da fuskantar koma-baya''. In ji editan littafin.
-
Wannan kuma sunansa 'Ko wuya ko dadi ', wanda Mr Okereke ya dauka a Legas a shekarar 2004. Mr Okereke, mamba ne na wata kungiyar samu tattara hotunan zamani, da aka kafa a Bamako a shekarar 2001. Littafin na dauke da hotunan biyu daga cikin masu zane-zane, watau George Osodi da Adolphus Opara, wadanda a halin yanzu suke wajen bikin nuna hotuna da ake gudanarwa a Mali.
-
Wannan kuma wasu hotunan ne a game da yadda wasu mutane ke rayuwa a karkashin gada, wanda Uche Okpa-Iroha, wani mai fafutikar yaki da cutar koda ya wallafa. Mr Uche yanke shawarar shiga sana'ari daukar hotuna ne bayan daya kalli wasan Depth of Field a shekarar 2005 Mr Okpa-Iroha, mutumin da a baya ke wayar da kan jama'a game da illar ciwon koda, kuma yanzu ya zama mai daukar hotuna bayan da aka yi bikin nunin hotuna a shekarar 2005. A halin yanzu yana jami'ar Rijksakademie van Beeldende Kunsten da ke Amsterdam don samun horo game da yadda ake daukar hotuna.
-
Photo 09: Ms Atawodi, wadda ta kwashe shekaru hudu tana shirya littafin hotunan, ta shaidawa BBC cewa za a bayar da kwafen littafin kyauta ga dakunan karatu da cibiyoyin bincike. A cewarta, "Ya samu karbuwa fiye da yadda muke zato". Wannan hoton mai suna 'Surviving Dreams' Andrew Esiebo ne ya dauke shi.
-
Mista Esiebo ne kuma marubucin littafin 'Members Only', wanda ya yi bayani da hotuna a kan mai tsaron kofar wani gidan kulob. Ya fara rubuta shi ne bayan wata mujalla ta nemi ya yi mata aiki a kansa. A cewarsa, "Lokacin da na samu wannan dama na yi tunanin cewa hanya ce mai kyau ta duba rayuwar talakan Najeriya".
-
Sunan wannan hoton, na Amaize Ojeikere, 'Dr Know All'. Ya yi aiki a kan jerin hotuna har kashi biyu - 'clusters' da 'The Market Place' - a kan abubuwa masu kama da juna. "Ba na so a bayyana ni a matsayin mai daukar hoton wurare ko mai daukar hoto ga jarida. Mai daukar hoto mai daukar hoto ne", in ji shi.
-
Wannan hoton da ba shi da suna Yetunde Ayeni-Babaeko, wacce ta karanci dabarun daukar hoto a Jamus sannan take shugabantar wani kamfanin tallace-tallace a Lagos, ita ta dauke shi. A ra'ayinta kakagidan da maza suka yi a harkar daukar hoto a Najeriya na raguwa. A cikin littafin ta ce: "Matan da ke zuwa wajena don koyon daukar hoton sai karuwa suke yi".











































