bbc.co.uk navigation

Hotuna: Ma'aikatan jirgi Mata-Maza a Thailand

An sabunta: 16 ga Disamba, 2011 - An wallafa a 15:05 GMT

Hotuna: Ma'aikatan jirgi Mata-Maza a Thailand

  • Kamfanin PC Air lokacin zirga-zirgarsa ta farko a cikin gida
    Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Thailand PC Air ya fara aiki tare da masu lura da fisinjoji Mata-Maza. Jigilar farko da ya yi ita ce daga birnin Bangkok zuwa gundumar Surat Thani a ranar Alhamis 15 Disamba, 2011. Shugaban kamfanin PC Air Peter Chan (na 3 daga hagu) ya dauki hoto tare da ma'aikatan jirgin Mata-Maza.
  • Kamfanin PC Air lokacin zirga-zirgarsa ta farko a cikin gida
    'Yan kasar Thailand Mata-Maza da ke kula da ayyukan cikin jirgi, daga hagu zuwa dama, Chayathisa Nakmai, Dissanai Chitpraphachin, Nathatai Sukkaset da kuma Phuntakarn Sringern a filin saukar jiragen sama na Bangkok.
  • Kamfanin PC Air lokacin zirga-zirgarsa ta farko a cikin gida
    Daya daga cikin ma'aikatan PC Air Mata-maza Nathatai Sukkase, 'yar shekara 26 da Phuntakarn Sringern, 'yar shekara 24, suna tallafawa fasinjoji a jirgin PC Air.
  • Kamfanin PC Air lokacin zirga-zirgarsa ta farko a cikin gida
    Daya daga cikin Mata-Maza da ke aiki a kamfanin jirgin sama na PC Air Chayathisa Nakma na gabatar da bayanan tsaro ga fasinjoji.
  • Kamfanin PC Air lokacin zirga-zirgarsa ta farko a cikin gida
    Kamfanin ya sauya shirinsa na dibar ma'aikatan cikin jirgi maza da mata a farkon bana, bayan da ya samu bukatar neman aiki fiye da 100 daga Mata-Maza, inda aka debi hudu daga cikinsu tare da mata 19 da kuma maza bakwai.
  • Kamfanin PC Air lokacin zirga-zirgarsa ta farko a cikin gida
    Kamfanin ya ce sharudan daukar aikin daidai su ke da na mata, inda ake bukatar su kasance kyawawa.
  • Kamfanin PC Air lokacin zirga-zirgarsa ta farko a cikin gida
    Wani jami'i na share fuskar wata ma'aikaciyar jirgi Mata-Maza Dissanai Chitpraphachin, a lokacin da ake koya musu yadda za su yi kwalliya a kamfanin na PC Air.
  • Kamfanin PC Air lokacin zirga-zirgarsa ta farko a cikin gida
    Ko wadannan ma'aikatan jirgin Mata-Maza za su taimaka wajen kawo sauyin da kamfanin na PC Air ke bukata?

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.