A cikin shirin na wannan makon za ku ji cikakken bayani a kan cutar Noma, watau zaizaiyar baki. Cutar dai tana kama yara ne masu shekaru 2 zuwa 6. Galibi dai rashin tsaftar baki ne ke janyo ta.
Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Wasu ma'aikatan asibiti
A cikin shirin na wannan makon za ku ji cikakken bayani a kan cutar Noma da ke zaizaiyar baki. Cutar dai tana kama yara ne masu shekaru 2 zuwa 6.
Galibi dai rashin tsaftar baki ne ke janyo cutar ta Noma, wadda ke fara kama dasashi , daga nan kuma sai kwayoyin cutar su samu shiga, har ciwon ya habaka, ya shafi duka bangaren fuska.
Dr Bashir Abduklkahi Jabo, shugaban Asibitin kula da masu cutar zaizayyar baki dake Sokoto, shi ne ya yi wa wakilinmu na Sokoto, Haruna Shehu Tangaza karin bayani a kan cutar ta Noma.
BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.
Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.