BBC navigation

Taho-mugama a dandalin Tahrir

An sabunta: 21 ga Nuwamba, 2011 - An wallafa a 15:57 GMT
  • Ma'aikatar lafiya ta kasar Masar ta tabbatar da mutuwar mutane ashirin da biyu, da kuma raunata wasu kusan dubu daya da dari takwas, a ciki kwanaki biyun da aka kwashe ana dauki-ba-dadi tsakanin masu zanga zanga da jami'an tsaro, a Alkahira, babban birnin kasar Masar.
  • Sojoji da 'yan sanda sun rika harbi da harsasai na roba, a kokarin tarwatsa masu zanga zangar da suka yi dafifi a dandalin Tahrir, dandalin da a can ne aka shirya gangamin da yayi sanadiyar kifar da gwamnatin shugaba Mubarak a watannin baya.
  • Masu zanga zangar na korafi ne cewar sojoji na kara yin babakere kan harkokin mulki, suna bukatar jagoran sojan da ya sauka.
  • Haryanzu akwai daruruwan masu zanga zanga a dandalin, kuma ana cigaba da samun rohotannin tashin hankali.
  • Gwamnatin dai ta ce za ta ci gaba da shirinta na gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki, wanda za a gudanar a makon da ke tafe.
  • Ta yi kira ga jam'iyyun siyasar kasar da su taimaka wajen ganin an daina zanga-zangar da ake yi.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.