BBC Hausa

Shafin Farko > News

Ana dab da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta! Inji Masar

Facebook Twitter
19 Nuw 2012 20:17 GMT
Hare-haren Israila a Gaza

Isra'ila da kungiyar Hamas sun bayyana sharuddan yin sulhu, yayinda Isra'ilar ke ci gaba da kai harin bamabamai a Zirin Gaza, su kuma Palasdinawa ke ci gaba da harba rokoki cikin Isra'ila.

Praministan kasar Masar Hisham Qandil wanda ke jagorantar wani yunkurin shiga tsakani, ya ce mai yuwuwa ana dab da cinma tsagaita wuta.

Jagoran kungiyar Hamas, Khalid Mish'al ya bukaci a kawo karshen abin da ya kira cin zaluncin da Isra'ila ke yi, da kuma killacewar da ta yi wa Zirin Gaza.

Jami'an gwamnatin Isra'ila sun ce suna da sharudda hudu da suka hada da , daina kai hare haren rokoki daga Gaza, da kuma kasashen duniya su sa ido domin ganin Hamas ba ta kara tara makamai ba.

Sojojin sama da na Ruwan Isra'ila sun kai hare-hare kusan 80 a yau kadai, ciki har da wani hari na biyu da suka kai kan wani gini da gidajen jaridar Gaza da na kasashen waje ke amfani da shi:

An dai tabbatar da mutuwar daya daga cikin mambobin kungiyar Islamic Jihad a yayin harin.

Jami'an Isra'ila sun ce masu tada kayar bayan Falasdinu sun harba rokoki da dama a kudancin Isra'ila lamarin da ya haddasa wasu mutane suka samu raunuka.

Duk da cigaba da rikicin da ake, har yanzu ana kokarin sasantawa a Alkahira babban birnin Masar akan batun tsagaita wuta.

Jagoran kungiyar Hamas Khalid Meshaal wanda yana daga cikin masu tattaunawar, ya dora alhakin tada sabon rikicin akan Isra'ila, a saboda haka ya ce dole ta tsagaita wuta

Sai dai kuma jami'an Isra'ila sun ce za su tsagaita wuta ne idan masu tada kayar bayan suka daina kai musu hari, sannan kuma kasashe su yi kokarin ganin cewa Hamas bata sake samun makamai ba.

Yair Lapid dan siyasa ne a Isra'ila ya ce duk da cewa ada ana ganin kamar wanda bashi da karfi shi ake cuta, amma a wannan karon an samu akasi.

Tunda farko dai, wani babban jami'i a Masar ya ce, akwai alamun za a samu nasara a tattaunawar da ake ta tsagaita wuta, kuma ta yiwu a bada sanarwar hakan nan gaba kadan.

Tura wannan bidiyon

Email Facebook Twitter