BBC Hausa

Shafin Farko > News

Babban Bankin Najeriya zai fito da takardar Naira dubu biyar

Facebook Twitter
24 Agu 2012 08:56 GMT
Kudin Najeriya

Babban bankin Najeriya CBN ya bada sanarwar cewa zai fito da sabuwar takardar kudi ta naira dubu biyar a cikin jerin kudaden kasar da ake hada hadar kasuwanci dasu.

A cewar babban bankin, sabuwar takardar kudin da ake shirin fitowa da ita a shekara mai zuwa za ta kasance dauke ne da hoton fuskokin wasu fitattun mata uku a Najeriya wato Margaret Ekpo da Hajia Gambo Sawaba da kuma Funmilayo Kuti.

Babban bankin na Najeriya ya ce, a yanzu za a sauya wa takardun kudi na naira 50, da naira 100, da naira 200, da naira 500, da naira 1,000 fasali, sannan a samar da sabuwar naira 5,000.

Kananan kudi da suka hadar da naira 5, da naira 10, da naira 20 kuma duk za a mayar da su tsaba.

Bankin na CBN din dai ya jaddada cewa yana kuma da burin kara inganta yanayin da fasalin kudaden da ake da su, domin kara musu karfi da daraja da kuma tsaro.

Wannan matakin in ji CBN zai saukaka yawan kudaden da ake kashewa wajen bugawa da fitar da takardun kudaden.

Babban Bankin dai ya bayyana cewa zai farfado da amfani da tsabar kudaden da yanzu haka suka bace daga cikin hada hadar kasuwancin kasar.

Ya kuma ce za a gwamutsa amfani da sabbin takardun kudin da wadanda ake da su a yanzu, inda sannu a hankali za a janye tsofaffin takardun, don haka ba sai jama'a sun yi gaggawar canza kudaden nasu ba.

Sai dai an sha yin gardandami game da yadda samar da sabbin manyan takardun kudin ke yin mummuna tasiri ga tattalin arzikin kasar, dama rage darajar kudaden kasar, lamarin da Babban Bankin ke musantawa.

Tura wannan bidiyon

Email Facebook Twitter