BBC navigation

Ra'ayi Riga: Yaki da cutar Polio a Afrika

An sabunta: 25 ga Mayu, 2012 - An wallafa a 20:54 GMT

Garmaho

Hukumar lafiya ta Duniya ta soma gudanar da wani gangamin gaggawa dake da aniyar kawar da cutar Polio. Har yanzu dai Polio na ci gaba da kasancewa a kasashe uku wato Nijeriya da Pakistan da kuma Afghanistan

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

Ra'ayi Riga: Yaki da cutar Polio a Afrika

Kasashe uku ne kawai suka rage da cutar Polio a duniya

Hukumar lafiya ta Duniya ta soma gudanar da wani gangamin gaggawa dake da aniyar kawar da cutar Polio.

Yunkurin ya zo ne yayin da ministocin kiyon lafiya suka hallara a Geneva domin taron kiyon lafiya na duniya na shekara shekara, ta hanyar ayyana cutar ta Polio a matsayin wata annobar da ta shafi duniya baki daya.

Har yanzu dai Polio na ci gaba da kasancewa a kasashe uku, wato Nijeriya da Pakistan da kuma Afghanistan,to amma kwararru kan kiyon lafiya sun damu da bullar cutar a kasashen da a da suka kawar da ita.

To domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato baki da suka hada da:

Dr Mohammed Ali Pate, Minista a Ma'aikatar lafiya ta Najeriya da kuma Comrade Ibrahim Jibril, Shugaban Shirin kula da lafiya a matakin farko na kasa reshen Jihar Sokoto da Malam Rabi'u Musa, Jami'in hulda da jama'a na ofishin hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya -- UNICEF -- a wasu jihohin arewacin Najeriya.

Akwai kuma Aminu Tudun Wada, Shugaban Kungiyar mutanen da Cutar Shan Inna ta Polio ta Nakasa. Haka nan kuma ta wayar salula muna tare da wasu daga cikinku, ku, masu saurarenmu.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.