BBC navigation

Ra'ayi Riga: Taron kasashen duniya kan Somalia

An sabunta: 24 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 20:55 GMT

Garmaho

Burtaniya ta ce an cimma matsaya kan batutuwan da suka shafi tsaro da fashin jiragen ruwa da ayyukan jinkai a taron da aka gudanar kan makomar kasar Somalia.

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

Ra'ayi Riga: Taron kasashen duniya kan Somalia

Somalia na fama da matsaloli iri daban-daban da suka hada da karancin abinci

Shekaru sama da ashirin kenan da ake ta fama da rikici a Somalia, tun bayan hambarar da gwamnatin Siad Barre a 1991, wadda ake zargi da fifita haularsa ta Darood.

Tun daga wannan lokacin ne kuma haulolin Somaliyar suka shiga zaman 'yan marina, kasar ta kasance bata da gwamnatin tsakiya, illa gwamnatocin rikon kwaryar da ba sa kai labari, saboda rarrabuwar kawuna.

An sami kungiyoyin tawaye da dama a Somaliyar - a yanzu mafi girma ita ce Al-Shabaab mai fafatawa da gwamnatin wucin-gadin Somaliyar, wadda kuma a kwanan nan ta kulla kawance da kungiyar Al Qaeda.

Gwamnatin Burtaniya bata gayyaci Al Shabaab din ba a taron London da aka shirya kan makomar Somaliyar.

Can kuma a gabar tekun Somaliyar, 'yan fashi a teku na ta cin karensu ba babbaka, yayin da suke kama jiragen ruwa don neman kudin fansa.

Sannan kusan mutane miliyan biyu da rabi na fama da yunwa a kasar, inda dubbai ke zaune a sansanonin gudun hijira, a kasashe makwabta.

Bakin da muka gayyato a shirin sun hada da: Farfesa Djibo Hamani, malami a jami'ar Abdulmuninu Dioffo dake birnin Yamai da Dr. Abubakar Sadik, Malami a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Sai kuma Sheikh Usman Bari, tsohon jami'in diplomasiyya, kuma masanin siyasar Afirka da yankin gabas ta tsakiya, wanda ke birnin Accra an kasar Ghana.

Akwai kuma Alhaji Ahmed Gulak, mai ba shugaban Najeriya shawara ta fuskar siyasa, a ofishinmu na Abuja.
Muna kuma tare da masu sauraro da yawa ta wayar tarho.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.