A ranar Lahadi ce mabiya addinin Kirista a ko'ina cikin duniya ke bukukuwan Kirsimati na bana. Ana bukukuwan ne domin tunawa da ranar Haihuwar Yesu Kiristi. A kasashen Afrika a kan gudanar da bukukuwan ne ta hanyar shirya abinci iri-iri.
Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Ana bikin Kirsimati a sassa da dama na duniya
A ranar Lahadi ce mabiya addinin Kirista a ko'ina cikin duniya ke bukukuwan Kirsimati na bana. Ana bukukuwan ne domin tunawa da ranar Haihuwar Yesu Kiristi.
A kasashen Afrika irin su Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Ghana, a kan gudanar da bukukuwan ne ta hanyar shirya abinci iri-iri.
Da sanya sabbin tufafi a tafi mujami'u domin yin addu'o'i, da kai ziyara ga gidajen 'yan uwa da abokan arziki.
To ko ya kirsimatin ta bana ta zo wa jama'a, wadanne irin abubuwa ya kamata a rika yi a lokacin bukukuwan kirsimati, kuma wadanne darussa ya kamata a koya a daidai irin wannan lokaci?
Wasu kenan daga cikin irin abubuwan da za mu tattauna a kansu a filinmu na Ra'ayi Riga na wannan makon.
Domin gabatar da shirin mun gayyato baki daban-daban cikinsu harda Rev. Ibrahim Usman a Katsina, Najeriya, sai kuma ku masu sauraro dake kan layi.
BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.
Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.