bbc.co.uk navigation

Ra'ayi Riga: Kalubalen da ke gaban shekara ta 2012

An sabunta: 30 ga Disamba, 2011 - An wallafa a 21:32 GMT

Garmaho

A ranar Lahadi ne za a shiga sabuwar shekara ta 2012, shekarar 2011 dai ta kasance mai dunbin kalubale ga wasu da dama. Ko menene fatan ku a sabuwar shekarar?

Sauraremp3

Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Kunna wannan da wata manhajar ta daban

Yaya za a tunkari shekarar 2012

An dai fuskanci kalubale da dama a shekarar 2011

Muhimman abubuwa da dama ne dai suka faru a wannan shekara mai karewa: An yi zaben shugaban kasa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.

A cikinta ne kuma Sudan ta kudu ta samu 'yanci. Sai dai kuma shekarar ta zo da kalubale.

Baya ga tsadar rayuwa a wurare da dama, rashin tsaro ya kasance wata babbar matsala da ke ci wa jama'a da mahukunta tuwo a kwarya a kasashe kamar su Najeriya.

Menene hasashen ku akan matsalolin da kuke jin za a iya fuskanta a shekara mai zuwa, kuma ta yaya za a bullo masu, kana kuma mene ne fatanku?

Wasu kenan daga cikin irin abubuwan da muka tattauna kan su a filin namu na Ra'ayi Riga na wannan makon.

Za mu ji ra'ayoyinku kai tsaye ta waya, akan wannan batu, baya ga wadanda za su bayyana ra'ayoyin nasu ta facebook ko ta email da wayar salula.

Domin tattaunawa kan wannan batu mun gayyato Barrista Ahmed Gulak Mai bai wa shugaba Goodluck na Najeriya shawara ta fuskar siyasa.

Akwai kuma Abubakar Kari, malami a jami'ar Abuja kuma mai sharhi akan al'amurran yau da kullum.

A Nijar kuma za mu ji daga Moussa Tchangari wani mai sharhi akan al'amurran yau da kullum.

Akwa kuma Kalla Moutari Mataimakin Babban Sakataren fadar shugaban kasar Nijar, kuma muna tare da su ne ta waya.

BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.