Ba ka da manhajar flash player da ta dace

Yayinda ake shirin fara azumin watan Ramalana, wasu abubuwa da jama'a suka fi kuka da shi a lokacin azumin shi ne batun tsadar kayayyakin abinci da sauran na masarufi.
Shin wane shiri jama'a suke yi na tunkarar azumin na bana, kuma wadanne irin darussa ake koya a lokacin azumin?
Wasu kenan daga cikin abubuwan da zamu tattauna kan su a shirinmu na Ra'ayi Riga na yau.
Baya ga ku masu sauraro dake kan layi, wasu daga cikin bakin da muka gayyato sun hada da Sheikh Ibrahim Khalil, wani malami a Kano, da Alhaji Kabiru Hali, shugaban kungiyar 'yan kasuwa na jihar Sokoto, da kuma Alhaji Sama'ila Hatim Mai'aya, shugaba 'yan kasuwa na Nijar.
A yi sauraro lafiya.
BBC © 2012 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.
Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.