|
Labarun Duniya
|
|||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
A kowace rana, Sashen Hausa na BBC yana watsa labarun duniya na akalla tsawon minti biyar a harshen Hausa a lokuta kamar haka:
0530 da 0630 da 1345 da 1930 agogon GMT.
Haka nan kuma, a kowace rana, akwai takaitattun labarun duniya na tsawon minti uku a shirye-shiryenmu na karfe 0530 da 0630 agogon GMT. Akan kama shirye-shiryen Sashen Hausa na BBC a kan mitoci kamar haka. Labaru da Rahotannin yau da kullum. Galibin shirye-shiryen Sashen Hausa na BBC suna kunshe da labarai da rahotanni na yau da kullum ne. Wakilan BBC a sassa daban-daban na duniya sukan aiko da rahotanni a kan muhimman abubuwan da ke faruwa a duniya, tare da labarai na abubuwan da ke faruwa a Nigeria da jamhuriyar Niger. Akwai labarun duniya na tsawon akalla minti biyar a cikin kowane shiri da Sashen Hausa na BBC ke watsawa. Daga ranar Litinin har zuwa ranar Juma'a, dukkanin shirye-shiryen sashen Hausa na BBC, suna dauke da rahotanni daban-daban a kan labarun yau da kullum, na akalla tsawon minti ashirin. Labarin wasanni A ranakun Litinin da Laraba da Juma'a, akwai labarin wasanni a shirin karfe 1930 agogon GMT. Muna kuma dauke da labarin wasannin a shirinmu na 0630 agogon GMT a ranakun Litinin zuwa Juma'a. Daga Jaridun Nigeria. Ranar Litinin a shirin karfe 0530 agogon GMT, akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da Jaridun karshen mako na Nigeria suka wallafa. Daga Jaridun Kasashen Duniya Ranar Talata a shirin karfe 0530 agogon GMT akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da jaridun wasu kasashen duniya suka wallafa. Ranar Laraba a shirin karfe 0530 agogon GMT akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da jaridun jamhuriyar Nijar suka wallafa. Ranar Alhamis a shirin karfe 0530 agogon GMT akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da jaridun kasar Kamaru suka wallafa. Ranar Juma'a a shirin karfe 0530 agogon GMT akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da jaridun kasar Ghana suka wallafa. Za a iya tuntubar mu a wannan addreshin na email: hausa@bbc.co.uk |
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||