| IKON MALLAKA | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Dukkan wani iko, har da ikon mallaka, na abin da ke cikin shafunan intanet na BBC, bisa wannan dalili, mallaka ne ko iko na BBC. Bisa shiga shafunan intanet na BBC, ka amince ke nan cewa za ka debi abin da ke ciki ne kawai don amfanin kanka ba wai ciniki ba. Ba a ba ka iznin kwafa, watsawa, diba, adanawa (ta kowace irin hanya), aikawa, nunawa ko sanya wa jama’a su ji, ko kwaskwarima ko sauyawa ta kowace irin hanya, abubuwan da ke cikin wannan dandalin intanet na BBC, bisa kowane irin dalili, ba tare da samun izni a rubuce ba daga BBC. BAYANIN KARE SIRRI Manufar Kare Sirri Wannan sanarwa tana bayanin manufarmu a kan bayanan da muke samu game da kai. 1. Bayanin Aniya 2. Bayani a kan maziyarta 3. Minene sàwu (cookie)? 4. Gabatar da bayanai game da mutum 5. Damar samun bayanai game kanka 6. Maziyarta ‘yan 16 da kasan haka 7. Yadda za gano da kuma iko da sawunka 8. Yaya za ka san shafunan da ke amfani da sawu? 9. Yadda za ka ga tsarin sirrin sawunka 1. Bayanin Aniya Daga lokaci zuwa lokaci, za a nemi ka bada bayani game da kanka (misali, sùna da adireshin email da sauransu) domin ka iya karba ko yin amfani da sassan da ke dandalimmu. Irin wadannan sassa sun hada da kasidu, da gàsa, da Sakon Gaggawa (Alert Email), da tattaunawar kai tsaye, da allon sakonni da kuma zama mamba na BBCi. Bisa shigar da bayaninka a wuraren da aka nema, to ka bà da dàma ke nan ga BBC da masu daukar nauyin shafunanta, na su ba ka ababen da ka zaba. A duk lokacin da ka ba da irin wannan bayani game da kanka, to za mu yi aiki da bayanin ne kamar yadda wannan manufa ta tsara. An tsara sassanmu ne yadda za su ba ka irin bayanin da kake bukatar samu. BBC za ta yi komi kamar yadda dokokin yanzu suka tsara, tare da nufin samar da mafiya kyawon hanyoyin samar da intanet na yanzu. 2. Bayani a kan maziyarta A lokacin ziyararka zuwa BBCi, shafunan da ka gani, hade da abin da ake kira sawu, za su shiga cikin kwamfuta dinka (duba bayani na 3 don kari a kan haka). Galibi, idan ma ba dukkani ba, na shafunan intanet, suna yin haka, sabo da sawu din ne ke ba da dama ga wanda ke wallafa dandalin na intanet ta yin muhimman abubuwa kamar su sanin ko kwamfutar (ko kuma mai amfani da ita) ya taba ziyartar shafin a can baya. Ana yin hakan ne a wajen sake kawo ziyara domin dubawa a ga, da kuma gano, sawun da ka bari a ziyararka ta baya. Duk wani bayanin da sawu ya bari, zai iya taimaka mana wajen inganta aikin da muke yi maku, ya kuma taimaka mana wajen sanin irin mutanen da ke kawo mana ziyara. Alal misali, idan a wata ziyara ta baya ka je shafunammu na ilmi, to muna iya fahimtar haka daga sawunka, mu kuma tuna maka bayanin da ya shafi ilmi idan ka dawo a wata ziyara ta biyu. RedSheriff, kamfanin lissafi da bincike mai zaman kansa, yana tara bayanan da basu shafi mutum ba shi kansa game da maziyartan shafukammu a madadimmu, ta hanyar amfani da wasu hikimomi da ke kunshe a shafin. Duka sawun da kuma hikimar sirrin da ke kunshe, suna bayar da bayanan kididdiga game da maziyarta shafunan da ke dandalin, da tsawon lokacin da suka kwashe a shafin, da bayani a kan tsarin aikin allon kwamfutar da sauran bayanai iri-iri. BBC tana amfani da irin wannan bayani, da kuma wanda aka samu daga wajen wasu sawayen da aka yi amfani da su a dandalin, don taimakawa su inganta ayyukan da ake gabatarwa ga masu amfani da dandalin. Idan kana son kin amincewa da sawu na RedSheriff, za ka iya amfani da hanyoyin da aka tsara a kasa a lamba ta 7. Idan kana son hana hikimar da aka tsara a ciki ta yi aiki, to sai ka aika da bukatar haka kai tsaye ga privacy@redsheriff.com. Za a iya samun karin bayani game da bayanin kare sirri na RedSheriff a http://www.redsheriff.com/6.0.0.htm. 3. Minene sàwu? Da ka shiga wani dandali, kai tsaye zai baiwa kwamfutarka sawu. Su sawaye fayiloli ne masu rubutu da ke ba da bayanin kwamputarka ga uwar kwamputocimmu. Shi kansa sawu bai bai iya gane kowane maziyarci, sai dai kwamfutar da aka yi amfani da ita. Dandaloli da dama sukan yi haka a duk lokacin da wani ya ziyarci dandalin domin su iya sanin yawan shiga da fita. Bakin abin da sawu ke yi shi ne fahimta kawai ta sassan da kwamfutar da ake magana a kanta ta ziyarta, da kuma tsawon lokaci. Maziyarta suna da dàmar tsara kwamfutocinsu yadda za su iya karbar dukkan sawu, ko su sanar da su idan ana neman a bi sawunsu, ko kuma su ki karba. Ko shakka babu, wannan batu na karshe na nufin ke nan maziyarcin ba zai sami wasu bukatu da za a ware don biya masa ba. LURA: Ko da ba ka sanya kwamfutarka ta ki karbar sawu ba, duk da haka. za ka iya shiga dandalimmu ba tare da ka bayyana kanka ba har sai lokacin da ka yi rajista don anfanuwa daga ayyukan BBCi 4. Gabatar da bayanai game da mutum Idan ka gabatar da wani bayani game da kanka ga BBCi (misali, domin gasanni, ko ayyukan Al’umma na BBCi, ko kuma zama mamba na BBCi) muna da hakki na doka a kan yadda za mu yi tu’ammali da wannan bayani. Lalle ne mu tara bayanan ta hanyar da ta dace, wato, lalle ne mu bayyana yadda za mu yi amfani da shi (duba sanarwowi a wasu shafukan intanet da za su ba ka damar sanin dalilin da suka sa muke neman bayanin) mu kuma gaya maka ko muna son tura bayanin ga wani. Galibi, duk wani bayanin da ka baiwa BBC, za a yi amfani da shi ne kawai a BBCn da kuma masu kular mata da intanet. Ba za a taba bayar da shi ba ga wani a waje da BBC in ba an nemi izninka ba, sai dai in ya zama wajibi a kammu ko muna da izni na doka na bayyana shi. Sannan kuma, idan ka sanya, ko turo wani abu na batunci ko wani abin da bai dace ba a ko’ina a BBCi, kuma BBC ta ga wannan abu rashin da’a ne ko kuma aka maimaita, BBCn za ta iya amfani da kowane irin bayanin da take da shi game da kai don dakatar da irin wannan halayya. Wannan zai iya hadawa da bayanin da ya shafi wani, kamar wanda kake ma aiki, ko makaranta ko kuma wani mai aikin sama wa jama’a adireshin email, game da abin da ka turon ko kuma game da halinka. Za mu ajiye bayananka a na’urorimmu iya lokacin da ka yi amfani da abubuwan da ka nema, mu kuma fitar da shi idan har wannan bukata ta riga ta biya, ko kuma idan kai mamba ne na BBCi, ka ji ba ka son cigaba da zama mamban na BBCi. Sai dai kuma, don kare lafiya, BBC za ta iya ajiye rubutu na wani sako (ciki har da abin da ke cikin sakon, rin su sunaye, da lokuta da kuma ranaku) wadanda aka sàmu ta hanyar amfani da Ayyukan Al’umma na BBCi, kamar su “Connector” na tsawon watanni shidda. A inda aka ajiye da bayanin mutanen da ba su riga suka yi rajista ba, amma sun shiga cikin wasu abubuwan na BBCi (misali, gasanni), za a ajiye wannan bayani ne iya tsawon yadda ya zama dole don tabbatar da cewa an yi aiki ba tare da tangarda ba. Za mu tabbatar da ganin duk wani bayanin mutum da ya bayar, an yi masa tsaro na kwarai, kamar yadda Dokar Kare Bayanai ta 1998 ta tanada. Idan aka sanar da kai a wani dandali na BBCi cewa za a iya amfani da bayanai game da kai don BBC ta iya tuntubarka don “bukatar tafiyar da ayyuka”, hakan na nufin mai yiwuwa BBCn ta tuntube ka bisa dalilai daban-daban da ke da ababen da ka yi rajistar kana bukata. Misali, za mu iya son tuna maka kalmarshiga, ko mu sanar da kai an dakatar da wani sashe don yin garambawul. Ba za mu tuntube ka don tallata wani abu ba, kamar su gaya maka cewa an inganta wani sashe ko sabbin sassa a BBCi, sai dai idan takamaimai ka amince a tuntube ka domin irin wadannan abubuwa a lokacin da ka gabatar da bayananka a dandalin, ko kuma daga baya idan ka yi rajista ta musamman don samun bayanan na tallatawa. 5. Damar samun bayanai game kanka 6. Maziyarta ‘yan 16 da kasan haka Idan shekarunka 16 ne ko kasa da haka, sai ka nemi iznin iyaye/masu kula da kai tukuna a duk lokacin da ka ba da bayanai game da kanka a dandalin intanet na BBC. Masu amfani da shafunammu ba tare da wannan iznin ba, ba a yarda su ba mu bayanai game da kansu ba. 7. Yadda za ka gano da kuma iko da sawunka Idan kana amfani da Netscape 6.0: Idan kana amfani da Internet Explorer 6.0: Idan kana amfani da Internet Explorer 5.0 or 5.5: Idan kana amfani da Internet Explorer 4.0: 8. Yaya za ka san shafunan da ke amfani da sawu? Idan kana amfani da Internet Explorer 5.0 or 6.0: Idan kana amfani da Internet Explorer 4.0: Internet Explorer 3.0: Netscape Communicator 4.0: 9. Yadda za ka ga tsarin sirrin sawunka British Broadcasting Corporation © 2001-2002 |
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||