02 Yuni, 2004 - An wallafa a 14:43 GMT
A kowace rana, Sashen Hausa na BBC yana watsa labarun duniya na akalla tsawon minti biyar a harshen Hausa a lokuta kamar haka: 0530 da 0630 da 1345 da 1930 agogon GMT.
Haka nan kuma, a kowace rana, akwai takaitattun labarun duniya na tsawon minti uku a shirye-shiryenmu na karfe 0530 da 0630 agogon GMT.
Akan kama shirye-shiryen Sashen Hausa na BBC a kan mitoci kamar haka.
Labaru da Rahotannin yau da kullum.
Galibin shirye-shiryen Sashen Hausa na BBC suna kunshe da labarai da rahotanni na yau da kullum ne.
Wakilan BBC a sassa daban-daban na duniya sukan aiko da rahotanni a kan muhimman abubuwan da ke faruwa a duniya, tare da labarai na abubuwan da ke faruwa a Nigeria da jamhuriyar Niger.
Akwai labarun duniya na tsawon akalla minti biyar a cikin kowane shiri da Sashen Hausa na BBC ke watsawa.
Daga ranar Litinin har zuwa ranar Juma'a, dukkanin shirye-shiryen sashen Hausa na BBC, suna dauke da rahotanni daban-daban a kan labarun yau da kullum, na akalla tsawon minti ashirin.
Labarin wasanni
A ranakun Litinin da Laraba da Juma'a, akwai labarin wasanni a shirin karfe 1930 agogon GMT. Muna kuma dauke da labarin wasannin a shirinmu na 0630 agogon GMT a ranakun Litinin zuwa Juma'a.
Daga Jaridun Nigeria.
Ranar Litinin a shirin karfe 0530 agogon GMT, akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da Jaridun karshen mako na Nigeria suka wallafa.
Daga Jaridun Kasashen Duniya
Ranar Talata a shirin karfe 0530 agogon GMT akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da jaridun wasu kasashen duniya suka wallafa.
Ranar Laraba a shirin karfe 0530 agogon GMT akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da jaridun jamhuriyar Nijar suka wallafa.
Ranar Alhamis a shirin karfe 0530 agogon GMT akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da jaridun kasar Kamaru suka wallafa.
Ranar Juma'a a shirin karfe 0530 agogon GMT akwai takaitaccen bayani a kan abubuwan da jaridun kasar Ghana suka wallafa.
Za a iya tuntubar mu a wannan addreshin na email: hausa@bbc.co.uk