Zaben Najeriya 2011

An sabunta: 14 ga Maris, 2013 - An wallafa a 11:49 GMT

Sakamakon zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi da aka gudanar a Najeriya, ya nuna cewa jam'iyyar PDP mai mulkin kasar na samun gagarumar nasara a jihohi da dama na kasar.

Babban mai shigar da kara na kotun hukunta laifukan yaki ta kasa-da kasa ICC ya ce kotun tana binciken ko an aikata laifukan yaki a rikice-rikicen da suka biyo bayan zaben shugaban Najeriya.

Wannan taswira ce ta musamman kan zaben Najeriya, wacce ke kunshe da bayanai kan al'amuran da suka shafi tattalin arziki da siyasa da lafiya da kuma ilimi.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta dage zabukan gwamnonin jihohin Bauchi da Kaduna daga Talata ashirin da shida zuwa Alhamis ashirin da takwas ga watan Aprilu.

Rikicin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a Najeriya, ya nuna irin abubuwan da ka iya faruwa a kasar, ganin yadda bangarorin jama'a ke ci gaba da nisantar juna ta fuskoki dabam-daban.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya yi wa 'yan kasar jawabi, inda ya ce tura ta kai bango, kuma daga yanzu gwamnati ba za ta saurarawa masu tayar da fitina a kasar ba.

Karin labarai

Karin labarai

Kundin Dokar Zaben Najeriya

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.