|
Shugaban Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Ron Gourlay ya ce kungiyar ta na duba yiwuwar, sayarda sunan filin wasanta na Stamford
Bridge ga wani kamfani.
A cikin wata hirar shi ta farko da yayi da manema labarai bayan ya maye gurbin Peter Kenyon, Mista Gourlay ya ce duk wata
yarjejeniyar sayarda sunan zai yiwu ne idan an samu wani babban kafani mai martaba.
Mista Gourlay ya bayyana cewar, ya na la'akari da mahimmacin da sunan filin wasan ta Stamford Bridge ga magoya bayan kungiyar
kwallon kafan, abinda kuma ya sa ba zai yarda a sauya sunan ba.
|