|
Dan Wasan Chelsea, Joe Cole ya ce dolene Chelsea ta lashe gasar Champions League ta Turai, muddin ta na so ta shiga cikin
sahun manyan kongiyoyin kwallon kafa da suka yi fice a Turai.
"Chelsea tana gina kanta domin zama shaharariyar kungiyar kwallon kafa kamar su Manchester United da Real Madrid da kuma AC
Milan, amma bazai tabbata ba inda bata lashe gasar Champions League ba". Inji Joe Cole.
Chelsea dai tayi fice a wasanin da ta buga a gasar Champions League ta wanan kakan wassanin, inda ta lashe duga wasanin da
ta buga kawo yanzu.
|