Shafin Farko / Ƙa’idojin aiki

Gaskiya da rashin kuskure

Rashin kuskurenka shi ne ƙashin bayan martabarka a matsayinka na ɗan jarida. A matsayinka na ɗan jarida kana da wata amincewa ce da masu sauraronka cewa za ka gano abu, ka kuma zo ka faɗa masu gaskiyarsa. Kana yi masu alƙawari ne cewa ba za ka yaudare su ba. In ba ka sani ba, ka ce ba ka sani ba. In kuma ka yi kuskure ka nemi gafara, ka kuma gyara.