Shafin Farko / Ƙa’idojin aiki

Doka

'Yan jarida suna buƙatar cikakkiyar fahimtar doka da yadda ta shafi aikinsu - ciki har da ɓata suna, da ikon mallaka, da tsare sirrin jama'a da kuma yin rahoto daga kotu.Wannan ba cikakken jagora ba ne, don haka lalle koyaushe 'yan jaridar BBC su nemi takamaimiyar shawara daga lauyoyin BBC a kan abin da ya shafi doka.