Riƙon amana

Aikin jaridar da bai yi la’akari da cewa aikin amana ne ba, bai wuce nishaɗi ba – ana kuma iya cewa – sam ma ba aikin jarida ba ne.

Riƙon amana

‘Yan jarida suna aiki ne bisa amana – ko sun ƙi ko sun so.

Kasancewa ɗan jarida a kowace kafar watsa labarai yana tattare da ɗaukar nauyin haƙƙin jama’a – duka ga waɗanda ke sauraronka  da sauran al’umma.

Aikin jaridar da bai yi la’akari da cewa aikin amana ne ba, bai wuce nishaɗi ba – ana kuma iya cewa – sam ma ba aikin jarida ba ne.

Aikin jarida na BBC yana da nauyin musamman a kansa na sauke haƙƙin jama’a. Da kuɗin jama’a ake tafiyar da shi – a Biritaniya, daga kuɗin lasin talabijin da jama’a ke biya – don haka lalle dukkan ‘yan jaridar BBC su yi shirin bai wa masu sauraronsu ba’asi a kan shawarwarin da suke aiki da su.

‘Yan jaridar BBC suna da wani nauyin kuma, na yin aiki domin mafi rinjayen jama’a da ke da buƙatu mabambanta, da al’adu da asali mabambanta, da kuma matakai mabambanta na yadda suka damu da manyan labarai na ranar.

BBC kan yi haka ta hanyar:

 • ba da rahoto ƙarara kuma kai tsaye na irin salon da ya dace da wannan ma’aikata
 • ba tare da raina masu saurare ba
 • ƙoƙarin bayyana abin da ya faru, da dalilin muhimmancinsa, da yadda za a fahimce shi ta hanyar bayyana shi don jan hankalin masu saurare.
 • sanin cewa akwai haƙƙin ba da ba’asi ga jama’a a kan shawarwari da zaɓi na aikin jarida da aka yanke shawara a kai
 • gyara kurakurai da kuma neman ahuwa a kansu

Sanin cewa akwai haƙƙin jama’a a kai ba wai yana nufin hakan ya kasance jagora ba ko kuma kawai yin irin aikin jaridar da jama’a ke son gani ko ji.

Ba kuma yana nufin guje wa yanke wata shawara ba.

Sai dai, yana nufin iya ba da gamsasshen dalilin shawarwarin aikin jaridar da ka yanke. Da kuma yin haka ta hanyar da za ta shawo kan su kansu masu sauraron da ba su amince da shawararka ba, su amince cewa kana da ƙwaƙƙwaran dalili a kan shawarar da ka yanke.

Kuma waɗannan dalilai sun dace da ƙa’idojin aikin jarida na BBC.

Kurakurai

Babu wata kafar labarai – babu wani ɗan jarida – da ke yin komi daidai a koyaushe.

Duk iya ƙoƙarin da ka yi na yin komi daidai, bisa adalci, ba nuna bambanci, za ka iya yin kuskure idan ka gamu da ƙurewar lokaci ko kuma bisa cewa lalle sai ka ba da labari kafin sanin cikakken bayani.

Shawarar da aka yanke a cikin rashin isasshen lokaci; wani nufi da aka bayyana a daidai ƙaratowar wa’adi; wani abin da aka saka wanda bai nuna ruhin abin da aka ce ko ake nufi ba.

A wajen ‘yan jarida da dama, cewa ‘a gafarce ni’ ya fi komi wuyar faɗi. Sai dai kuma kasancewa cikin shirin neman ahuwa nan da nan, kuma ba tare da wani zuƙe-zuƙe ba idan ka yi kuskure, wani ɓangare ne na gina amana da kuma tabbatar da ita.

Ka sani

‘Yan jarida, kamar kowa, suna koyon darasi daga kurakurai. Idan ka kasa amsa yin su da kuma ba da gamsasshen ba’asi a kansu, ba za ka koyi darasi daga gare su ba.

BBC ma’aikata ce da ake gudanar da ita da kuɗaɗen jama’a, don haka ‘yan jaridar BBC, fiye da kowaɗanne ‘yan jarida, akwai bukatar su tambayi kansu:

‘Me za ni sa ran ganin aukuwarsa idan na yi ƙorafi ga wata hukumar da jama’a ke biyan kuɗin gudanar da ita – hukumar da nake biyan nawa kuɗin wajen gudanar da ita?’

Aƙalla, za ka sa ran samun bayani. Idan kuma kuskure aka yi, za ka sa ran neman ahuwa.

Zai fi kyau – musamman ma a kan labaran kai tsaye da ke ci gaba da gudana ko kuma a shafin yana – ‘yan jarida su gyara kurakurai da zaran sun fahimci yin su. Jama’a sun fahimci labarai suna shigowa ne da kaɗan-kaɗan, don haka, sau da yawa ba za a rasa illa ba a kan bayanai da kuma fahimta na farko-farko.

A ɗaya ɓangaren , yanzu labari ba na ɗan lokaci ba ne – wato labarin jiya. Shafukan yana, labarai a na’urori, labaran da aka alaƙanta da wasu, da dai sauransu, na nufin galibin aikin jarida ya koma na yanzu-yanzu har abada. Haka su ma kurakurai.

Ƙorafi

Idan har ka sami wani ƙorafi, muhimmi ne ka:

 • Tunkare shi bisa duk wata ƙa’idar ƙorafi da aka tsara – ka tuna hakan zai kuma kare ka daga ‘yan yawan ƙorafin
 • Maida amsa cikin natsuwa da ladabi ko da kuwa da wane irin lafazi ne aka yi ƙorafin – kada ka aika da imel ko yin kira ta waya cikin gaggawa
 • Dinga yi wa mai ƙorafin bayanin halin da ake ciki – idan za ka yi binciken gaskiyar batun ne, faɗi hakan. Kuma ka faɗi lokacin da kake sanya samun sakamakon bincikenka
 • Idan mai ƙorafin yana da gaskiya, faɗi hakan ba tare da ƙumbuya-ƙumbuya ba, ka kuma nuna abin da za ka yi game da hakan
 • Idan mai ƙorafin ne ya yi kuskure ko kuma akwai bambancin ra’ayi na gaskiya, faɗi hakan, tare da faɗin dalilin da ya sa ka yin amannar cewa kana da gaskiya
 • Rubuta tare da adana abin da kuka tattauna – mai yiwuwa batun ƙorafin ya ƙara tsanani.