Shafin Farko / Ƙa’idojin aiki

Riƙon amana

‘Yan jarida suna aiki ne bisa amana don masu sauraronsu da sauran al’umma. Lalle su yi aiki domin mafi rinjayen jama’a da ke da buƙatu mabambanta, da al’adu da asali mabambanta. Su kuma mutunta masu sauraronsu wajen ba su rahotannin da suka dace, yadda ya dace, ba kurakurai ko son zuciya, tare da ba da haƙuri da kuma yin gyara in an yi kurakuran.