Shafin Farko

Ƙa’idojin aiki

BBC tana da ƙa’idojin da take aiki da su, waɗanda suka haɗa da riƙon amana, da gaskiya da rashin kuskure, da rashin nuna bambanci, da lura da buƙatun jama’a da kuma ‘yanci. A wannan ɓangaren mun duba yadda waɗannan ƙa’idoji suka kasance ƙashin bayan aikin da BBC take yi ne na watsa labarai. Mun kuma ba da misalai a kan irin yadda ake aiki da waɗannan ƙa’idoji.