Manyan haruffa

Babban baƙì ake amfani da shi a farkon kowace kalma ta sunayen muhimman wurare kamar su Sashen Hausa na BBC, da Majalisar Dinkin Duniya, Gidan Talabijin na ‘Yanshuni.

Manyan haruffa

A rubutun Hausa akwai kalmomi da dama da in an zo rubuta su, wajibi ne harafinsu na farko ya zama babban baƙì.A rubutun Hausa akwai kalmomi da dama da in an zo rubuta su, wajibi ne harafinsu na farko ya zama babban baƙì.

Ban da farkon jumla da kowa ya san cewa ana farawa ne da babban baƙi, akwai kuma kalmomi da dama da lalle ne harafinsu na farko ya kasance babba.

 

Suna

A koyaushe harafin farko na sunan mutum babban baƙì ne – shi kaɗai ne, tsura, ko kuwa a cikin jumla.

Misali:

Abu, Garba, Salisu, Ashiru.

Haka shi ma sunan Ubangiji:  Allah. Idan kuma aka yi amfani da wakilin suna game da Shi, to Shi ɗin ma da babban baƙi ne za a soma Shi.

Sunayen mala’iku ma da babban baƙì ake soma su.

 

Keɓantattun Sunaye

Sunayen da ake ba littafai, da mujallu, da jaridu, da finafinai da wasannin kwaikwayo ana fara kowane harafin farko a cikin sunan da babban baƙi.

A nan kalmomin da za a soma da babban baƙìn su ne: suna, wakilin suna, siffa da kuma aikatau, amma ban da harafin haɗau da na wuri.

Misalai:

Littafi: Iliya Dan Mai Karfi, So Aljannar Duniya, Kulɓa Na Ɓarna

Fim:                 Ɗiyar Sarki Tana Son Ɗan Talaka, Gobara daga Kogi

Wasan Kwaiwayo:      Kiɗin Ganga da Lauje, Zanga-zangar ‘Yan Garin Gòga

 

Wurare

Babban baƙì ake amfani da shi a farkon kowace kalma ta sunayen muhimman wurare  kamar su Sashen Hausa na BBC, da Majalisar Dinkin Duniya, Gidan Talabijin na ‘Yanshuni.

Unguwanni:       Darma, Saulawa, Makudawa.

Ƙauyuka da Birane:         Sakkwato, Katsina, Kano, Tsabawa,

Kasashe:              Najeriya, Nijar da Kamaru, Chadi, Biritaniya.

 

Lokuta

Da babban baƙì ake soma sunayen ranakuL         Jumma’a, Litinin, Alhamis.

Haka su ma sunayen watanni:    Rajab, Ramadan, Shawwal, Janairu, Agusta.

 

Bukukuwa

Bukukuwa irin su Idil Fidiri, da Babbar Sallah da Kirsimati, haruffansu na farko manya ne.

 

Addinai

Sunayen addinai, Islam, Musulunci, Kiristanci, Yahudanci - duka harafin farko na kalma ko kalmominsu manya ne.

 

Muƙàmi

Idan aka haɗa muƙami da sunan mai muƙàmin, to muƙàmin zai soma ne da babban baƙì – Shugaba ‘Yar’aduwa, Farfesa Isa Shehu, Malam Musa, Alhaji Idi Raɗɗa.