Shafin Farko / Harshe

Lanƙwasa da nuɗuƙi

Lanƙwasa ga wasu haruffa tana taimakawa wajen bambanta lafazinsu da na wasu masu kama da su. Shi ma nuɗuƙì, koda yake babu shi a ƙa’idar rubutun Hausa, rashinsa kan rikita mai karatu, ya saka shi cikin rashin tabbas game da lafazin kalma. Shi ya sanya ake yawan amfani da shi a ƙamus ko wani rubun na koyon Hausa.