Lanƙwasa da nuɗuƙi

Lanƙwasa alama ce da ake yi wa wasu haruffan Hausa don a faɗe su da lafazi dabam da ake kiran wasu haruffan masu kama da su. Matsalar rashin amfani da lanƙwasa a kan kalmomin da ya kamata su mallaki lanƙwasar shi ne yiwuwar kuskuren zaton waɗansu kalmomin ne daban aka rubuta maimakon waɗanda aka yi nufi.

Lanƙwasa da nuɗuƙi

Bari mu fara da batun lanƙwasa, wadda alama ce da ake yi wa wasu haruffan Hausa don a faɗe su da lafazi dabam da ake kiran wasu haruffan masu kama da su.

Hakan zai ba da dàmà wajen rubuta kalmomi waɗanda in ba da lanƙwasar ba ko kuma wani abu da ke wakiltarta, sai ya zama babu tabbas game da yadda ya kamata a karanta su.

 

Haruffan Lanƙwasa

Haruffan Hausa da ake wa lanƙwasa su ne: ɓ Ɓ, ɗ Ɗ, ƙ Ƙ.

A inda na’urar rubutun ba ta da hanyar yin haruffa masu lanƙwasa, akan yi amfani da nuɗuƙì a matsayin wakilin lanƙwasar kamar haka: ‘b ‘B, d’ ‘D, k’ K’.

 

Misalan amfani

Ana amfani da harafin lanƙwasa na ɓ wajen rubuta kalmomi irin su ɓarke, ɓaràwo, ɓauna, ɓàwo, d.s.

Ana amfani da harafin lanƙwasa na ‘ɗ’’ wajen rubuta kalmomi irin su ɗàki, ɗauka, ɗàri, ɗòkì, ɗàci, d.s.

Ana amfani da harafin lanƙwasa na ‘ƙ’ wajen rubuta kalmomi isin su lanƙwasa, ƙanè, ƙanwa, ƙaƙà, ƙaryà, ƙoƙuwa, d.s.

 

Matsalar rashin lanƙwasa

Matsalar rashin amfani da lanƙwasa a kan kalmomin da ya kamata su mallaki lanƙwasar shi ne yiwuwar kuskuren zaton waɗansu kalmomin ne daban aka rubuta maimakon waɗanda aka yi nufi.

Hakan zai haifar da kuskuren fahimtar saƙon da ake son isarwa.

Ko kuma a wajen karatu, za a iya yin nisa kafin a gane ashe abin da aka karanta a baya ba shi ake nufi ba.

Misali, idan ba a sanya lanƙwasa ba a harafin farko na kalmar ‘ɗòkì’ abin da ke nufin zumuɗi, za a iya ɗauka cewa ana nufin ‘doki’ ne, wato dabba, wadda ake hawa.

Ana iya daukar ‘ɓàra’ da ke nufin raba abu gida biyu a matsayin bàra, wadda ke nufin shekarar da ta wuce.

Matsalar hakan ta fi yawa a inda irin wannan harafi ya kasance a farkon jumla, abin da kan haifar da kwan-gaba-kwan-baya a wajen karanta labarai.

 

Nuɗuƙì

Wata matsalar da ake fama da ita a rubutun Hausa ta shafi yadda ya kamata a ja ko a gajarta lafazi a kan wasu kalomomi.

A halin yanzu, in banda a cikin ƙamus ko littafin koyar da Hausa, ba a faye samun wata alama ba da za ta nuna maka gaɓar da za ka ja a kalma ko ka gajarta, da kuma ko jan na baya ne ko kuma na gaba. Nuɗuƙì shi ne mafita.

Shi ya sa akan yi amfani da shi a ƙamus ko kuma littafin koyon Hausa don kawar da irin rùɗun da muka yi magana a kai a sama.

Misali, idan na rubuta ‘Ka koma’ ba tare da na sanya nuɗuƙì ba, sai ka rasa shin ina nufin: ‘Kà kòma’ ne ko ‘Ká kòma?’ ko kuwa ‘Ka kòma’.

A nan, nuɗuƙì yana iya warware maka zare da abawa.

Don haka, sanya nuɗuƙìa kan kalmomi masu haruffa iri guda, zai kawar da kokanto a game da shin ko wace ce daga cikin kalmomin ake nufi a abin da aka rubutan.