Siffa da wakilin suna

Mai karatu zai iya yi maka ragguwar fahimta game da saƙon da kake son isarwa. Zai iya fara karanta su tare da zaton tambaya ce ka fara yi, wadda sauran kalmomin da za su biyo baya za su kammala ta.

Siffa da wakilin suna

Haɗe ko rabe? 

Kalmomi wakilan sùna ko siffa suna da hanyoyi da ƙa’idar rubutun Hausa ta amince a rubuta su.

Ba daidai ba ne ka rubuta: ko wane, ko waɗanne, ko mai, ko yaushe, ko ina in ba tambaya kake yi ba.

Mai karatu zai iya yi maka ragguwar fahimta game da saƙon da kake son isarwa.

Zai iya fara karanta su tare da zaton tambaya ce ka fara yi, wadda sauran kalmomin da za su biyo baya za su kammala ta.

Misali:

‘Ko wane mutun ne zai shigo?’, ‘Ko waɗanne mutane ne suka zo?’, ‘Ko mai rigar nan fara malami ne?’ ‘Ko yaushe Ali zai zo?’, ko kuma, ‘Ko ina Musa ya nufa?’.

Sai bayan ya kwaso karatun ne sai ya ga wani waje dabam jumlar da yake karantawa ta nufa ba inda ya zata ba.

Don haka, idan kana nufin kalmomi ne da za a iya amfani da su a matsayin siffa ko wakilin suna kamar haka: ‘Kowane mutum mai mutuwa ne’, ‘An miƙa wa kowaɗanne mutane rabonsu.’ ‘Komai ya yi daidai’, ‘Suna zuwa nan koyaushe’, to duk haɗe su za ka yi kamar yadda muka haɗe su a cikin waɗannan misalai.