Shafin Farko

Harshe

Yin amfani da nahawun harshe, da ƙa'idar rubuta shi da la'akari da al'adun masu harshen suna inganta fahimta da amincewa daga masu sauraro. Wajen amfani da harshen Hausa, yana da kyau kwarai misali, ka yi amfani da lanƙwasa a kan haruffan da ke buƙatar lanƙwasar don raba su da masu kama da su. Ka kuma yi amfani da kalmomin da galibin masu sauraren ka za su fahimta, ba na garinku ko ƙauyenku kawai ba. A takaice, yi amfani da daidaitacciyar Hausa.


Sassa

Lafazi

Furta lafazi dadai yana da matuƙar muhimmanci ga dukkan ‘yan-jarida don tabbatar da fahimtar rahotanni ba kuskure. Waɗanne hanyoyi ne ake cim ma hakan?

Ƙalubalen Harshe

Akwai ƙalubale da yawa a fagen watsa labarai. Da yake kuma sana’a ce ta magana, ita kuma magana zarar bunu ce, ƙalubalen da ke kan mai maganar shi ne na dacewar furucinsa ta fuskoki daban-daban.

Sunayen Ƙasashe da Manyan Birane

Ko ka san yadda ake rubuta sunayen ƙasashe da manyan biranen duniya da Hausa? To haƙa ta cim ma ruwa. Wannan sashe ya samar da su.

Nasaba da mallaka

Hanyar rubuta dangantaka ko mallaka ta kasu kashi biyu - doguwa ko gajera. Sulaiman Ibrahim Katsina ya bayyana yadda ake amfani da su daidai don inganta fahimta.

Siffa da wakilin suna

Kuskure ne ka rubuta: ko wane, ko mai, d.s. in ba tambaya kake yi ba. Mai karatu zai iya yi wa saƙonka ragguwar fahimta. Sulaiman Ibrahim Katsina ya fadi dalili

Mufuradi da jam’i

Kar ka ba da sigar mufuradi ga jam’i ne. Kar kuma ka ba da sigar jam’i ga mufuradi. Sulaiman Ibrahim Katsina ya bayyana illar hakan

Manyan haruffa

Ga Sulaiman Ibrahim Katsina da bayanin kalmomin da dama da in za a rubuta su wajibi ne harafinsu na farko ya zama babban baƙì.

Manunan lokaci

Ga Sulaiman Ibrrahim Katsina da misalin yadda ake rubuta jumloli na aikatau bisa la’akari da lokcin aukuwar lamarin da suke magana a kai.

Lanƙwasa da nuɗuƙi

Lanƙwasa ga wasu haruffa tana taimakawa wajen bambanta lafazinsu da na wasu masu kama da su, in ji Sulaiman Ibrahim Katsina

Jinsi

A daidaitacciyar Hausa, duk wani abin da yake sùna ne a nahawunce yana da jinsi na namiji ko kuma mace. Ga hanyoyin rage kuskure

Haɗau

Yaya ake amfani da kalmomin haɗa wani bangare na jumla da wani ko wasu, ko kuma haɗa wata jumlar da wata?