Shafin Farko / Yadda ake aikin

Aiwatar da ayyuka

Lalle mu yi tunanin yadda za mu zaɓi hotunan da suka fi dacewa don sakawa a yana. Lalle ne kuma mu ɗauki hotunan bidiyo irin yadda za su isar da saƙo a mafi kyawon hanya. Mu kuma tabbatar mun tantance hotunan da masu saurare suka aiko mana don tabbatar da ingancinsu da sahihancinsu kafin sakawa a yana don kada a bar baya da ƙurà.

Yadda Za a Ba da Laraban Olampik

Yayin da ake ta ƙara samun bazuwar fasahohi da hanyoyin sadarwa sabbi, yaya za ka iya yin rahotannin Wasannin Olampik da ake kira abin kallo mafi girma a duniya? Editar Wasanni a BBC ta yi ƙarin bayani.

Yadda za ka yi nasara a YouTube

Kate Rushworth ta yi bayanin hanyoyin da za ka bi don bidiyonka ya yi nasara a YouTube.

Yadda Ake Rubuta Rahoto

Rubuta rahoto yana buƙatar fahimtar muhimmancin labarin da za ka yi rahoton a kai da kuma matakan da suka kamata ka ɗauka wajen rubuta shi yadda zai gamsar, in ji Mansur Liman, tsohon Editan Sashen Hausa na BBC.

Yadda ake Tantance Gaskiyar Labari da Kare Majiyoyi

Labarai suna buƙatar ɗaukar matakai don tabbatar da ingancinsu? Jimeh Saleh, Muƙaddashin Editan Sashen Hausa na BBC, ya yi ƙarin bayani a kan yadda ake yin hakan, har ma da yadda za a yi da wanda bai son a bayyana sunansa.

Aikin Jarida ta Wayar Salula: Sauti

Ɗaukar kyakkyawan sauti da haziƙar waya (wayar komi-da-ruwanka) sam bai da wuya idan ka bi wasu sharuɗɗa masu sauƙi. Ƙwararre a kan haziƙar waya, Marc Settle, ya bayyana yadda za ka ci gàjiya sosai ta wayar salula kamar iPhone.

Aikin Jarida ta Wayar Salula: Hotuna

Ɗaukar kyakkyawan hoto da haziƙar waya (wayar komi-da-ruwanka) sam bai da wuya idan ka bi wasu sharuɗɗa masu sauƙi. Ƙwararre a kan haziƙar waya, Marc Settle, ya bayyana yadda za ka ci gàjiya sosai ta wayar iPhone da wasu wayoyin na salula.

Yin adalci ga waɗanda kake hira da su

Yin komi a bayyane kuma cikin ‘yanci suna cikin muhimman abubuwa wajen yin adalci ga waɗanda za ka yi hira da su. Lalle ne ka fayyace wa wanda za ka yi hirar da shi ko a kan wane batu ne za a yi hirar.

Yadda za ka ba da labari

A kowane mataki, daga shi kansa labarin zuwa yadda za ka haɗa hancin kowane ɓangare nasa wuri guda, zai yi shafi tasirin rahotonka.