Ƙa’idar hira da baƙì

Akwai hirarraki iri daban-daban, kowace kuma tana da tata hanyar da ake yin ta. Hirarrakin da aniyarsu ita ce su auna wata muhawara suna bukatar karfafan tambayoyi – bai yiwuwa ka bar wanda kake wa tambayoyin ya yi wa masu saurare wala-wala.

Ƙa’idar hira da baƙì

TAMBAYA:  Yaya za ka tabbatar ka yi wa baƙinka adalaci ko da hirarka da su mai tsauri ce?

Akwai hirarraki iri daban-daban, kowace kuma tana da tata hanyar da ake yin ta.Akwai hirarraki iri daban-daban, kowace kuma tana da tata hanyar da ake yin ta.

Hirarrakin da aniyarsu ita ce su auna wata muhawara ko kuma su nemi martini a kan wani zargi, sau da yawa akwai bukatar a yi su da karfafan tambayoyi – bai yiwuwa ka bar wanda kake wa tambayoyin ya yi wa masu saurare wala-wala.

A ɗaya bangaren kuma, ya kamata ka yi wa baƙon adalci.

Ka’idar Sir Robin

Kusan shekaru 50 baya, lokacin da masu watsa labarai ke fara sabawa da yin hirar da ke cike da ƙalubale, wani matashi mai suna Robin Day ya bayyana ra’ayin cewa:

“Mai watsa labarai yana da ‘yanci da kuma haƙƙin yin tambayoyi masu tsauri a madadin sauran al’umma.”

Sai dai mai tsauri ba tana nufin marar adalci ba.

c

Ga ka’idojin nasa:

  • Lalle mai yin hira a talabijin ya yi aikinsa na ɗan jarida, ya yi ta tambayoyin neman gane gaskiya da kuma ra’ayi
  • Ya ajiye son zuciyarsa a gefe, ya yi tambayoyi da za su wakilci ra’ayoyi daban-daban, ya kuma yi watsi da zargin nuna bambanci
  • Kada ya bari griman wani babban mutum ya cika masa fuska fiye da kima
  • Bai kamata ya lalata gaskiyar hirar ba, ta hanyar ƙin yin tambayoyi masu tsauri ko kuma ya ba da satar tambayoyin gabanin hirar
  • Kada ya yarda da buƙatar waɗanda yake yi wa aiki ta sassauta ko ba da satar tambayoyin don samun wata martaba ko daɗaɗa wa hukuma. Bayan ɗan jaridar ya nuna rashin amincewarsa, yana iya janyewa daga hirar
  • Bai kamata ya miƙa tambayoyinsa a gani kafin hirar ba, amma babu laifi idan ya bayyana muhimman batutuwan da zai yi hirar a kai. Idan har ya ba da tambayoyi a gani gabanin hira, to bai da sauran ƙarfin yin wasu karin tambayoyin, waɗanda wataƙila suna da muhimmanci wajen ƙara haske ko kuma ƙalubalantar wata amsa
  • Ya ba da lokacin da ya dace don ba da amsa bisa la’akari da iya lokacin da gidan talabijin ɗin ya bayar
  • Sam kada ya yi amfani da ratar ƙwarewar da yake da ita don yin tarko ko kunyata wani wanda bai saba bayyana a talabijin ba
  • Ya yi tambayoyinsa ba sani ba sabo, kuma ya nace amma ba har yadda za a gaji ba, ko ya kasance akwai mugun bàki, ko kuma kawai don a ji cewa ai shi ba dama ne
  • Ya tuna cewa mai hira da mutane a talabijin ba an ɗauke shi aiki ba ne a matsayin ɗan muhawara, ko mai gabatar da ƙara ba, ko mai binciken ƙwaƙwaf, ko mai binciken hankali, ko mai yin lalas don tatsar bayanai, a’a ɗan jarida ne da ke neman bayani a madadin mai kallo ko sauraro.

Ka’idar Robin Day, wadda ta yi batun yadda ake hira da ma yadda ake shirya ta, ta daɗe ba a daina aiki da ita ba, kuma ta shimfiɗa ka’idojin bi don yin hira mai kyau.

Duk da sunan da ya yi na mai hira mafi hazaƙa da kuma zafi, Sir Robin bai da lokacin yi wa mutane rijiya ko yaudara, ko wani abin daban in ban da adalci da kuma yin komi kai tsaye.

Su ma masu kallo ko saurare ba su da sha’awar haka. Da yawa daga cikin masu kallon BBC suna cewa suna sauya tasha idan suka ga hirar da suke kallo ba a yin ta irin yadda ya dace. Masu kallon da ya kamata su ji hirar a jikinsu, sai su rasa inda aka nufa da zaran hankali ya tashi daga wanda ake tambaya zuwa rashin kyautawar da ake yi masa.

Wasu masu sukar BBC suna muhawarar cewa rashin sani ko sàbo da wasu mashahuran masu yin tambayoyi ke nunawa, gaba ɗaya ya ma sauya yadda ake yin siyasa a ƙasar.