Shafin Farko / Yadda ake aikin

Gabatar da shiri

Gabatar da shiri yana buƙatar kyautata murya. Yi hakan ta shan ruwa a kai-a kai da kuma yin lumfashi a duk inda ya dace. Wajen hira da bako, yi ƙwararan tambayoyi - kada a yi wa masu saurare wala-wala. Shi ma baƙon, a yi masa adalci. Tsohon Editan Kwalejin Aikin Jarida, Kevin Marsh da gwana a sha’anin murya Elspeth Morrison sun nuna hanya.