Shafin Farko / Yadda ake aikin

Aikin jarida na hazaƙa

Aikin jarida aiki ne na ƙwaƙwalowa da gabatar wa jama’a sabon labari koyaushe. Yana buƙatar iya tallatawa a gaban edita don ya ba da iznin yin rahoton. Wajen rubuta shi kuma, akwai abubuwan la’akari don samun jan hankalin mai saurare. Kevin Marsh, tsohon Editan Kwalejin Aikin Jarida da Ian Winter, shi ma na BB,C sun yi ƙarin bayani.