Tallatawa da taruka

A matsayinka na mai tsara shiri ko ɗan rahoto, akwai buƙatar ka san maƙasudin kowane ɓangare na taro, ka shirya masa, ka kuma duba dukkan matakan da aka zayyana don shata yadda za ka ba da taka gudummuwa.

Tallatawa da taruka

Kana da shawarar wani sabon labari – abin da kawai kake buƙata shi ne yadda za ka tallata ta.

Galibi za ka yi hakan ne a wajen tarukan tsara shiri ko kuma tattaunawa. Kuma za su iya kasancewa sun kashe maka baki, wani lokaci, ko su ruɗa ka.

Wannan jagora game da shirya kanka ne yadda za ka iya tallata shawararka ta mafi kyawon hanya, ka yi mata adalci, da kuma yadda za ka cire wani abu daga cikin damuwar da kake da ita.

Haka kuma ya shafi yadda halayyarka za ta sauya yanayin waɗannan taruka, idan kuma kai ne ke jagorantar tattaunawar, yadda za ka taimaka wajen samar da kyakkyawan yanayin da zai taimaka wajen ƙago shawarwari na gari

Wannan taro a kan mine ne?

Galibin tarukan tsara shiri suna da ɓangarori biyu – ɓangaren aiki (sanarwa a kan sauya wa wasu wurare da matsayi da kuma a kan rahotannin da aka riga aka yi shiri a kansu suke kuma kan hanya) sai kuma abubuwan amfani da ƙwaƙwalwa wajen ganowa (kamar wasu fuskokin na labari, da sabbin shawarwari, da sabbin labarai, da sabbin mutanen da za a yi magana da su, da sauya salo).

Tarukan aiki

 • Ba su faye tsawo ba
 • Na ba da umurni ne, daga wani tsari da aka shirya a can baya
 • Yawancin tsoma baki tambayoyi ne
 • Galibin shawarwari a kan yadda za a warware wasu tabbatattun matsaloli ne
 • Sani yana da muhimmanci
 • Ana ƙarewa ne idan an samu cikakken tabbacin aiki ko ayyukan da za a kammala.

Tarukan ƙirƙiro shawarwari

 • Ba su da tsawo
 • Ba na ba da umurni ba ne, babu wani jerin abubuwan yi
 • Galibin tsoma baki ba da shawarwari ne, gabatar da abin da kake gani
 • Lokacin da za ka fara ba tilas ka san matsalar da kake son warwarewa ba...yawan abubuwan da suke shige duhu za su iya ƙaruwa daga wannan taro
 • Aƙalla muhimmancin tambaya a jahilce tamkar na tambaya da sani ne
 • Suna ƙarewa da sanin manyan abubuwa da ka yiwu amma babu tabbas.

Tarukan ƙirƙira suna buƙatar jin ƙarfi sosai, da kuma fuskantar abu fiye da ɗaya; su kuwa tarukan aiki suna buƙatar maida hankali sosai ne a kan abu guda.

Tarukan aiki game da kammala abin da aka riga aka saba ne; na ƙirƙira kuwa za su iya ɗaukar tsawon lokaci ba tare da sanin yadda kammala su za ta kasance ba.

Sani abin da ke aukuwa

A matsayinka na mai tsara shiri ko ɗan rahoto, akwai buƙatar ka san maƙasudin kowane ɓangare na taro, ka shirya masa, ka kuma duba dukkan matakan da aka zayyana don shata yadda za ka  ba da taka gudummuwa.

Idan kai ne ke jagorantar taron, lalle ka fito ƙarara ka bayyana abin da kake sa ran gani a kowane mataki na tattaunawar.

Idan taron na aiki ne, a yi shi babu ɓata lokaci; idan na ƙirƙirar dabaru ne, a nan jagoranci na gari ne ake buƙata.