Shafin Farko / Yadda ake aikin

Ba’asi a kan aiki

Bayyana ra’ayinka a kan aikin wani da kuma sauraron ra’ayin wani a kan aikinka, hanyoyi ne na ƙwarai na kyautata aikin jarida. Kar ka jinkirta faɗin gaskiyar abin da ka gani, ka kuma ba da dalili. Kada kai kuma ka kare naka aikin ƙarfi da ya ji in aka yi maka gyara, wai don kada a ce ka yi kuskure. In ka saurara za ka amfana, in ji Lucy King.