Sauraron yadda aka ga aikinka

Ka tabbatar ka fahimci ainihin abin da ake shaida maka. Ka kuma tabbatar mutumin da ke bayyana yadda ya ga wani aiki, to shi ma ya saurari abin da kai kuma za ka ce a matsayin maida jawabi.

Sauraron yadda aka ga aikinka

Yadda za ka saurari yadda ake ganin aikinka

Saurari

An faɗi abubuwa da dama a kan yadda za a bayyana yadda kake ganin aikin wani. Amma a akasin haka, abin da aka ce game da yadda kai kuma za ka saurari bayani a kan aikinka bai da yawa. Sai dai wannan abu ne kaifi biyu. Yadda mutum ya saurari, kana ya amshi abin da aka ce masa da yadda aka gabatar masa da shi, duka muhimmancinsu iri guda ne.

Lucy King ta BBC World Service ta ba da wannan shawara:

  • Saurari abin da mutumin ke ce maka
  • Yi tambayoyi don fahimta sosai
  • Nemi karin bayani sosai
  • Tambayi abin da za ka iya sauyawa a gaba

Kar ka kare kanka ƙarfi da yaji

Idan kana sauraren yadda aka ga aikinka, yi iya ƙoƙarinka kada kai ta kare kanka ƙarfi da yaji.

Wannan dama ce gare ka ta ƙara fahimtar kanka da kuma yadda wasu daban suke ganinka. Don haka, yi ƙoƙarin sauraron abin da mutane ke ce maka tare da aiki da shi.

Ka tuna, babu laifi ka tafi ka yi tunani a sosai a kan yadda ake bayyana ganin aikinka sannan ka yi tambayoyi daga baya.

Sararawa

Ba laifi ba ne ka nemi a dakatar da taro idan kana son samun lokacin yin tunani.

Yana da muhimanci ka maida jawabi, amma fa ka yi nazari sosai kafin ka maida jawabin.

Don haka, ka nemi a sake tattanawa bayan ka yi tunani, kà kuma sami lokacin yin nazarin abin da aka faɗa zuwa yanzu.

Ba ni gishiri in ba ka manda

Ka tuna cewa bayyana yadda ka ga aikin wani na buƙatar kai ma ka saurari ta bakinsa.

Ka tabbatar ka fahimci ainihin abin da ake shaida maka. Ka kuma tabbatar mutumin da ke bayyana yadda ya ga wani aiki, to shi ma ya saurari abin da kai kuma za ka ce a matsayin maida jawabi.

Da zaran ka tabbatar da fahimtarka a zuciyarka, ka iya tattauna abin da za a yi na gaba.

Tabbatar cewa

Ka fayyace ra’ayin da kake nema, ka kuma yi hakan a taƙaice. Don haka, idan kana neman jin ra’ayin wani, ka bayyana takamaiman abin da kake son sani.

Ka shaida wa wanda ke ba ka ra’ayinsa abin da kake son sani game da takamaiman ɓangare na aikinka.

Ta haka ne za ka sami amsoshi masu amfani, tabbatattu, ba kame-kame kuma game-gari ba.

Matakai na gaba

Daidaiton baki a kan abin da za a yi a gaba wani ɓangare ne na bayyana yadda aka ga aiki.

Watakila za ka bukaci taimako wajen aiwatar da abin da aka ankarar da kai, don haka tattauna abin da za a yi a gaba. Yi kuma tunani a kan samun:

  • Goyon bayan manajanka
  • Bayani a kai-a kai don nazarin ci-gaban da kake samu.
  • Horo ko kuma jagora

Yi aiki da abin da ke yiwuwa

Guji kwaɗayin alƙawarta abin da ya wuce misali. Lalle ku amince a kan abin da za a iya cimmawa, ba wai abin da ke da wuyar aikatawa ba.

Zayyana tsarin da dukkanku ke ganin cewa za ku iya cimmawa.