Bayyana yadda ka ga aiki

Bayyana ra’ayinka a kan aikin da aka yi ita ce mafi kyawon hanya ta kai wa ga aiki mai kyau. Kar kai ta jinkirta faɗin gaskiyar abin da ka gani tare da dalili. Bayani gaba-da-gaba ya fi na imel, ko waya, ko tes. Kai ma kuma, ka saurari ra’ayin wasu ko na ɗan rahoton don ƙaruwa da wani abu, in ji Lucy King.

Bayyana yadda ka ga aiki

Hanyar bayyana yadda ka ga aikin wani cikin matakai goma masu sauƙi

Ko da a ranar aiki ya yi maka yawa, muhimmin abu ne ka bayyana yadda kake ganin aikin ma’aikatanka. In ka lura, ai babbar buƙatarka ita ce ka watsa labarai ta hanyar da ta fi kyawo. Bayyana ganinka ɗin kuma ita ce mafi kyawon hanya ta cim ma hakan.

Don haka, ni ga abin da nake yi, ka jarraba shi ka gani.

 

Sirri na 1. Ko ba komi, a dai tattauna

Kada kai ta jinkirta faɗin abin da ka gani. Na san ba ka da isasshen lokaci, ba ka kuma da tabbacin abin da za ka ce. Sai dai ka tuna, idan ka daure ka yi nazarin aikin da wani ya yi a tsanaki, ka kuma faɗa masa gaskiyar abin da kake gani, zai matukar jin daɗin hakan. Ko da ba ka so, aƙalla dai ka saurara. Na tabbata karo na biyu zai fi na farko sauƙi.

 

Sirri na 2.  Bayyana ƙarara dalilinka na faɗin abin da kake ganin

Dalili ɗaya tal ne na bayyana wa mutane abin da kake gani game da aikinsu – shi ne kuwa cewa ita ce hanya mafi sauƙi ta taimaka masu su kyautata aikinsu. Babu shakka sabon ɗan jarida yana buƙatar bayani mai yawa a kan yadda aka ga aikinsa – ba shi da dukkan ƙwarewar da ake buƙata don samun ƙarfin gwiwa da ƙwarewa. Don haka, akwai buƙatar ka gaya masa abin da yake yi daidai da wanda yake kuskure a kai.

Sai dai haka ma abin yake ga ɗan rahoton da ya riga ya ƙware. Ba koyaushe ba ne zai yi yi daidai a kan rahoton da ya yi. Akwai bukatar editansa ya faɗa masa abin da ya yi daidan da wanda bai yi ba.

 

Sirri na 3.  Ka mallaki naka ra’ayin

Za ka so wani mutum na biyu ko ma na uku ya gaya maka abin da wani mutum na farko ya ce game da aikinka? Hakan yana yawan aukuwa. Kada kawai ka ce ga abin da edita na London ya ce maka. Kai ma ka sami naka ra’ayin, ka kuma faɗa masu ga abin da kake gani. Idan har ba ka amince da abin da wani edita ya ce ba, faɗi hakan. Ba da shawara na iya kasancewa ra’ayi ne kawai.

 

Sirri na 4.  Yabì abin da ke da kyau

Bayyana ganinka a kan aiki ba tilas ya warkar ba, amma muhimmiyar hanya ce ta ƙara wa mutane ƙwarin gwiwa. Don haka, ka yaba masu in ka ga sun yi aiki na gari, ko kuma sun yi namijin ƙoƙari. Kuma ka yi ba tare da ɓata lokaci ba, gaba da gaba ne, ko ta saƙon tes ko kuma na imel. Duk dai ta hanyar da za ka iya. Za ka ga amfanin hakan ne a gaba, a lokacin da ka buƙaci yin magana da ɗan rahoton game da wani abu da ya yi da bai tafi daidai ba, zai fi sauraronka da kunnen ƙwarai. Ka ga ka cin ma nasara ke nan.

 

Sirri na 5.  Fayyacè sosai

Da yabo da suka, duka dokarsu ɗaya ce – ita ce kuwa fayyace abin da kake nufi. Cewa : ‘Ya yi kyau...’ ko ‘Ni wannan bai yi mani ba’ bai wadatar ba.

Idan ka ce ya yi kyau, mine ne abin da ya sanya ya yi kyan? Idan kuma bai yi ba, mine ne ya hana shi yi? Watakila akwai bukatar ka sake duba aikin don gano dalili. Tsarinsa ne ba daidai ba? Ko kalmomin da aka yi amfani da su ne ba daidai ba?

 

Sirri na 6.  Nemi duk wata dama za ka iya samu ta bayyana ganinka a kan aikin wani

Yi amfani da dukkan damar da za ka iya samu, a hukunce ko a’a, wajen faɗin yadda ka ga aiki. Koyaushe, gaba da gaba ya fi kyau – zai iya kasancewa a mashigi ko a shagon abinci. Amma in kana ganin abin yana da ‘yar matsala , to ka tabbatar an yi hakan a keɓe. Idan har ɗan rahoton ba ya ofis, to ya fi kyau ka yi waya maimakon rubuta imel ko sakon tes. Amma ka yi tunanin ganawa ido da ido – za ka iya yin hakan wajen tattauna aikinsa na shekara. Sai dai yin hakan sau da yawa a shekara ya fi amfani.

 

Sirri na 7.  Tattaunawa

Ka yi shirin sauraro, ka kuma yi shirin ƙaruwa da wani abu. Mai yiwuwa ɗan rahoton ya san takamaiman abin da ya hana rahoton kasancewa yadda kowa ya so. Don haka, saurarar shi, yi masa tambayoyin da za su kai ga gane dalilinsa na yanke shawarar yin rahoton haka a lokacin. Ka kuma shirya ma ɗaukar alhakin hakan – mai yiwuwa kai ne ba ka fayyace masa abin da kake son ya yi ba sosai. Ya kamata ka dinga yin cikakken bayani. Ƙila ya kamata ka dinga binciike da wuri a kan yadda shirin rahoton ke gudana.

 

Sirri na 8.  Yi amfani da kujerar masu sauraro

Mai yiwuwa kana ganin rahoton bai yi ba, ka kuma san dukkan abin da ya faru game da labarin, to su kuma masu saurare fa, wadanda sau ɗaya za su ji ko su ga labarin? Za ka iya gwada wannan dabarar: ka nemi ɗan rahoton da ya nazarci rahoton tamkar karonsa ke nan na farko na jinsa. Sau da yawa zai gano inda kalaman rahoton suke da ruɗarwa da yawa ko kuma inda suka ɗauka masu sauraro sun san muhimman abubuwa game da labarin don haka ba su haɗa da su ba a rahoton.

 

Sirri na 9.  Yi tambayoyin da za su sanya su yin tunani

Idan kana son ɗan rahoto ya yi rahoto mai kyau, to ka sanya shi ya yi tunani a kan duk shawarar da zai yanke yayin da yake haɗa labarin. Don haka, yi masa tambayoyi masu sauƙi. Wadda na fi sha’awa it ace , ‘Mine ne labarin?’ Tàke sai ka ji ya sheda maka cikin jumla guda abin da yake yi ta faman faɗi a cikin rahoton da aka watsan.

Yi masa tambaya a kan abubuwan da ya zaɓi sanyawa a cikin rahoton da kuma abin da ya bari. Ta hakan ne za ka yi tattaunawa mai amfani a kan yadda ake ba da labari.

 

Sirri na 10.  Sami amincewa a kan tabbatattun ƙudurori, ka kuma binciki minene mai rahoto ke buƙatar ganin ya cim masu? 

Ku amince a kan abin da za ka so gani a yayin da yake gwada yin wani sabon abu, tare da cewa za ka bayyana masa yadda ka ga yadda ya gudanar da aikin.

Tambayi sauran editocin da ke aiki a shirin ko zai taimaka idan ka sanar da su kudurori da aka sa gaba shirin naka. Kàna ka tuna, aikin fa na taimaka wa mai rahoto ne don ya yi mafi kyawon aiki.