‘Yanci

Idan kana son a amince da kai, to ka tabbatar wa jama’a cewa kana da cikakken ‘yanci. Ya kamata ɗan jarida ya kare kansa daga buƙatun hukuma ko ƙungiya a wajen aikata kuskure. ‘Yanci ba cijewa ba ne ko zargin mutane ba dalili wai don ka nuna kana da ‘yanci.

‘Yanci

Idan kana son a amince da kai, ‘yancinka yana da matuƙar muhimmanci.

Ana iya kallon ‘yanci a matsayin abin da a fili ke da muhimmanci ga ‘yan jarida – sai dai mice ce amsarka ga waɗannan tambayoyi hudu?

  1. Kana da ‘yanci da kuma da alamar kare kanka daga buƙatun gwamnati, siyasa, kasuwanci ko kuma duk wani mai wata buƙata game da abin da kake ba da labari?
  2. Kana ƙin goyon baya, ko nuna alamar goyon bayan, duk wata ƙungiya, ko abin da take aiwatarwa, harkoki zuwa ayyukanta?
  3. Kana kauce wa yawan kwarzanta abin da wata ma’aikata ta ƙera ko ta fitar a shirinka?
  4. Shin lalle kà fahimci cewa harkokinka a waje da babban aikin da kake yi ba su da wani tasiri da bai dace ba a aikin jaridarka da kuma tsara shirye-shirye?

‘Yanci a zuci yake. Ba ɗaya yake da cijewa ba – ba kuma yana nufin ka dinga zargin aniyar kowa ba kawai wai don ka nuna kana da ‘yanci.

Bayyana ‘yancinka yana da muhimmanci kwatankwacin na mallakar shi kansa ‘yancin.

Alama

Mai yiwuwa ka yi zaton babu wanda ke shakkun ‘yancinka – kai fa ɗan jarida ne. Tabbas, BBC da mutanen da ke yi mata aiki masu ‘yanci ne; a ma iya cewa wani lokacin masu cijewa ne. Haka dukkan ‘yan jarida suke.

‘Yan jarida muna son ɗauka cewa:

‘Ba mu daukar umurni daga kowa. Mu ke yanke shawarmu a kan labaran da za mu ba da, haka kuma tsarin ba da labaran. ‘Yanci yana tafiya ne tare da amana da rashin nuna bambanci. Muna ba da rahoto ba tare da tsoro ko shayin wani ba. Iyakarta ke nan.’

Sai dai akwai wani tsohon kalami da ya ce: ‘Muna auna kanmu a kan niyyarmu, sauran jama’a kuma a kan abin da suka aikata.’

Yin tunanin kawai cewa kana da ‘yancin kanka – ko kana da nufi ko aniyar zama haka – sam ba su isa ba. Kuma hakan ba zai iya gamsar da kowa ba a cikin masu saurarenka cewa kana da cikakken ‘yanci.

Saboda nauyin da suke da shi game da masu sauraron su, lalle ne ‘yan jaridar BBC su iya nuna ‘yancin da suke da shi a shawarwarin da suke yankewa, kana su dinga yin iya kokarinsu wajen kawar da yiwuwar samun linkin ma’ana ko kokanto.

Idan kana da kokanto a kan dangantakar da kake da ita da wani da sunansa ke cikin labarai, tambayi kanka: ‘Yaya wani mutum daban zai kalli hakan?’ ko kuma idan wani a cikin masu sauraro ya san cewa gà ta irin hanyar da nake samun labarin, zai ɗauka ina da ‘yanci kuwa?’

Binciki kanka; anya ka nesanta kanka sosai daga yiwuwar samun wani tasiri a kanka?

Idan kakan yi tu’ammali da alamomi da aiwatattun kayayyaki – idan kai ɗan jaridar harkokin kasuwanci ne, alal misali – a fayyace take sosai cewa kana ba da rahoto ne a kan wannan abu ba kana ƙoƙarin tallata shi ba?