Manunan lokaci

Ana rubuta jumloli na aikatau bisa la’akari da lokcin aukuwar lamarin da suke magana a kai. Shuɗaɗɗen lokaci shi ne na abin da ya riga ya auku ko ya kasa aukuwa a can baya – ‘Na je’, ‘Kun ce’, ‘Sun karanta, ‘Ba ku je ba’, ‘Ba mu ce ba’. Daga abin da ke sama za a iya fahimta cewa kalmar wanda ya yi abu da kuma abin da aka yin rarraba su ake yi.

Manunan lokaci

Ana rubuta jumloli na aikatau bisa la’akari da lokcin aukuwar lamarin da suke magana a kai.

  

Shuɗaɗɗe

Shuɗaɗɗen lokaci shi ne na abin da ya riga ya auku ko ya kasa aukuwa a can  baya – ‘Na je’, ‘Kun ce’, ‘Sun karanta, ‘Ba ku je ba’, ‘Ba mu ce ba’.

Daga abin da ke sama za a iya fahimta cewa kalmar wanda ya yi abu da kuma abin da aka yin rarraba su ake yi.

 

Misali:

’Kà kyauta’, ‘Sun manta’, ‘Na rubuta’,’ Ka je’, ‘Kun duba shi’.

 

Ci gaba

Abin da ake cikin yi a halin yanzu, wato ba a kammala shi ba, ana amfani da wakilin suna ne da kuma ‘na’ a matsayin kalma guda, kana a bayyana aikatau ɗin da ake yin.

Misali:

‘Suna zuwa’,’ Kuna gani’, ‘Muna cin abinci’,  ‘Ina rubutu’, ‘Kina tunani’.

Sai dai idan za a kore abin da ake zaton ko za a iya zaton ana yi, to ana amfani ne da ‘ba’, sai wakilin suna, sannan aikatau,

Misali:

‘Bà nà zuwa’, ‘Bà kà kallo’, ‘Bà ya ƙoshi’, ‘Bà mu zuwa’, ‘Bà su motsawa’.

Har wa yau, wajen nuna abin da ake ci gaba da yi akwai wasu kalmomin da ake haɗa wakilin suna da ‘ke’ wajen rubuta su.

Misali:

Nake, kake, kike, yake, take, muke, kuke, suke.

A aikin da ya shuɗe kuma kalmomin za su iya komawa kamar haka: muka, kuka suka.

Misali:

Abin da kuka yi ya burge. Wanda suka suka gaisa da shi baƙo ne.

 

Sabau

Sabau shi ne abin da aka sàba yi lokaci-lokaci. Shi ana haɗa wakilin suna ne da ‘kan’ a matsayin kalma guda kana a ambaci aikatau din.

Kalmomin za su kasance kamar haka ke nan: nikan, kakan, kikan, yakan, takan, sukan, mukan.

Misali:

‘Nikan je kasuwa’,’Kakan yi karatu’, Yakan yi noma’, ‘Takan yi surfè’, ‘Sukan sha fura’, ‘Mukan yi tàro’.

 

Gabá

Ana rubuta abin da za a yi a gaba ta amfani da ‘za’.

In kana magana game da kanka sai ka ƙara mata ‘n’. Idan kuma game da wani ko wasu kake magana, sai ka yi amfani da wakilin sunan da ya dace da shi bayan ita ‘za’ ɗin.

Misali:

‘Zan je’, ‘Za ka je’, ‘Za ki je’, ‘Za mu je’, ‘Za su je’, ‘Za shi je’, ‘Za ku je’.

Idan kana son nuna abin da ake zaton zai auku ba zai aukun ba, za ka yi amfani da ‘ba’ ne gabanin jumlar da kuma wata ‘ba’ ɗin a ƙarshen jumlar.

Misali:

Ba zan je ba. Ba za su karɓa ba. Ba za su daina ba. Ba za mu manta ba.