Jinsi

A daidaitacciyar Hausa, duk wani abu wanda yake sùna ne a nahawunce, yana da jinsi, na namiji ko kuma mace.

Sai dai a karin harshen wasu yankunan, ko da a ƙasar Hausa, babu cikakken bambancin jinsi.

Kawai sai ka ga an labta wa mace jinsin namiji, a kuma labta wa namiji jinsin mace ba tare da damuwa ba.

Amma a daidaitacciyar Hausa tilas ne a fayyace abu namiji ne ko kuma mace.

Misalai:

Mutane - dole a bambance tsakanin namiji da mace – maigida ne, uwargida ce, miji ne, mata ce, yaro ne, yarinya ce, bàƙo ne, bàƙuwa ce.

Dabbobi - su ma dabbobi idan an tabbatar da jinsi, dole ne a fayyace shi – kùra ce, kùre ne, giwa ce, giye/toron giwa ne.

A inda ba a iya bambancewa cikin sauƙi, akan ɗauki jinsi guda a kira su da shi.

Misali:

‘Na ga giwa ta wuce’, zai iya yiwuwa in an bincika sosai a ga giye ne ba giwa ba.

Ana kirari cewa ‘Kurà mabì dare’, abin da ke nufin duka kùra da kùre duk mabiya dare ne, amma kuma duka kùra ta wakilce su.

Zan iya cewa, ‘Na gasa kifi’, amma ai zai iya yiwuwa kifanya ce na gasa ba kifi ba. Duk da haka dai, babu laifi.

Duk wannan bai hana inda aka tabbatar abu jinsin namiji ne a liƙa masa ‘ne’ ba, mace kuma  a liƙa mata ‘ce’.

Akwai abin da ke taimakawa wajen gane ko kalma ta suna jinsin mace ce ko namiji.

Galibin kalmomi na sùna da suka ƙare da wasalin ‘a’ mata ne – mota, tàba,gaɓà, gadà, gambà, tuta, tasha, taska, kurna, magarya, wuta.

Amma akwai kaɗan da suka fita zakka.

Ga su da wasalin ‘a’ ɗin a ƙarshe amma jinsinsu na maza ne, irin su dilà, ɓèrà, watà, gida, bàyà, kàyà, gàyà, dumà, d.s.

Aikatau ɗin da aka mayar sùna mai ‘wa’ a ƙarshe, ‘wa’ ɗin yà mayar da jinsinsa na mace.

Misali:

ɗauka/ɗaukewa, sheƙa/sheƙawa, karanta/karantawa, fake/fakewa, amince/amincewa. ‘Daukewa ce, sheƙawa ce, karantawa ce, fakewa ce, amicewa ce.

Jam’i yana sauya galibin jinsi zuwa na namiji, in ban da inda ake nuna mazakuta.

Misali:

namiji = maza/mazaje

mace = mata/mataye.

Misali:

maza ne, mata ne, mataye ne.