Haɗau

Idan kana son haɗa abubuwa fiye da ɗaya a jumla guda, to za ka sa ‘da’ gabanin kowane, da wakafi a bayansa illa biyu na karshe. A kansu, ‘da’ ɗin ce kawai za ta haɗa su kamar yadda za mu gani.

Haɗau

Kalmomin haɗi suna haɗa wani bangare na jumla da wani ko wasu, ko kuma su haɗa wata jumlar da wata ko wasu, don tada jumla guda.

Irin waɗannan kalmomi suna da nasu ka’idojin na rubuta su.

‘Da’

Idan ka zo amfani da kalmar ‘da’ wajen haɗa wasu ɓangarori biyu na jumla, ‘da’ ɗin kawai za ka rubuta.

Misali:

Akwai jituwa sosai tsakanin harshe da haƙori.

Amma idan kana son haɗa abubuwa fiye da ɗaya a jumla guda, to za ka sa ‘da’ gabanin kowane, da wakafi a bayansa illa biyu na karshe. A kansu, ‘da’ ɗin ce kawai za ta haɗa su kamar haka: Shuka tana son ruwa, da tàki, da nòma da hasken rana.

 

‘Amma’/’sai dai’

Wajen amfani da ‘amma’ ko ’sai dai’ don sanya sharaɗi ko kokanto ga wata jumla da ta gabata, ana sanya wakafi ne a bayan jumlar ta farko.

Misali:

Ya sayo masa riga, amma shi ya fi son hula.

Ya gayyace shi yin dara, sai dai shi ba ya son ɓata lokacinsa a wofi.

 

Wanda/wadda

Idan za ka yi amfani da ‘wanda’ ko ‘wadda’ don ƙarin bayani game da abin da jumlarka ke magana a kai, za ka yi amfani da waƙafi bayan kalmar da ta gabaci wanda/wadda ɗin, ka kuma sanya waƙafi bayan ƙarin bayanin, sannan ka kammala jumlar.

Misali:

Abdulkarim, wanda ya zo jiya da yamma, soja ne.

Malamar makarantar nan, wadda ta yi jawabi jiya a wajen taro, haziƙa ce ƙwarai.