Rubuta taƙaitattun labarun rediyo

Idan ka fara aiki da wuri sosai, za ka samu isasshen lokacin komawa kan rahoton da ka gina labarin a kai, na kamfunnan dillancin labarai ne ko kuma abin da wakilinku ya rubuta.

Rubuta taƙaitattun labarum rediyo

Masu saurare

 

Yi tunani a kan wane ne ke saurare. Rubutun taƙaitattun labarai da za su dace da abin da tasha ke watsawa da kuma buƙatun masu saurare ƙwarewa ce da ake samu bayan iya aiki tsawon shekaru.

Matakin farko shi ne fahimtar waɗanda kake watsa ma shirinka, hakan yana da tasiri a kan irin labaran da za ka zaɓa.

 

 

Tsawon lokaci

To ko yaya za ka yi lissafin tsawon labarai da kuma taƙaitattun labarai?

Don rubuta labarai ko taƙaitattun labarai masu ban sha’awa da ke da salo, ka yi ƙoƙarin daidaita labarin da lokaci.

Abin da aka saba da shi shi ne, ka yi ƙoƙarin yin labarai biyar cikin minti biyu, shidda ko bakwai kuma a taƙaitattun labarai na minti ukku, inda za a ƙawata labarai biyu ko uku da wani sauti da ya shafi labaran.

Bai kamata wata murya da za a saka ta wuce daƙiƙa 35 ba.

 

Sake bi

Dalilin da ya sa za ka bi ka kuma sake bi.

Idan ka je wurin aiki, karanta ‘yan taƙaitattun labaran da aka riga aka yi domin ka san labaran da tasharka tai ta bayarwa – ka kuma lura ko an sami wani sabon labari.

Da zaran ka yanke shawarar labaran da kake son bayarwa, sai kuma ka tabbatar ka fahimce su.

Idan ka fara aiki da wuri sosai, za ka samu isasshen lokacin komawa kan rahoton da ka gina labarin a kai, na kamfunnan dillancin labarai ne ko kuma abin da wakilinku ya rubuta.

 

Sauƙi

Rubuta takaitaccen labari na nufin ka sassabe komi zuwa tsuran muhimman abubuwan da ke cikin labarin.

Nufin rediyo shi ne yin iya ƙoƙarin kusantar irin kalmomin da ake zance da su.

Don haka, ka auna kowace kalma a tsanake, ka kuma kauce ma maimaici, duka na kalmomin da kake amfani da su da kuma tafiyar tunaninka.

“Galibin labarai ana iya ba da su cikin jumloli biyu ko ukku – kuma lalle kowace ƙarin jumla ta kasance ɗauke da wani sabon abu,”

in ji Helen Morgan-Wynne

 

Sabuntawa

Ya kamata ka san yadda za ka dinga sabunta labari a duk tsawon wuni.

Idan labarin da ya ɗan daɗe ana yi ne, zai yi kyau idan ka ɗan ciyar da shi gaba – misali, da wani martini a kan labarin.

Mutane suna gundura sosai idan suka wuni suna jin labarai, suka kuma ji ana ta faman maimaita jumlolin wani labari.

 

Shawara

Ga shawarar Helen Morgan-Wynne ta ƙarshe, kuma kamar yadda take gani, wataƙila wadda ta fi kowace muhimmanci:

 “Idan har lokaci ya fara ƙure maka, nemi taimako. Kana aiki ne a matsayin wani ɓangare na ƙungiya guda, kuma kowa yana iya gamuwa da matsaloli.”