Samun murya mafi dacewa

Game da abin da ke da amfani, ruwa shi ne babban abokin aikinka. Koyaushe ka tabbatar kana yawan shan ruwa a duka tsawon wunin da kake watsa shiri ko kuma kake ɗaukarsa. Abubuwa kuma irin su hayaƙi, da gahawa, da wasu abinci ko magunguna, yi hankali da su.

Hanya mafi kyau ta amfani da muryarka

Makurofo da lumfashi.

Wasu dabarun amfani da makurofo za su tabbatar za a ji ka yadda kake kuma a natse.

Malamar murya Elspeth Morrison tana da wasu ‘yan dabarun kyautata yadda za ka yi amfani da makurofo.

Ta ce kada ka yi ƙoƙarin sanya makurufo din dab da bakinka, kamar yadda ka ga mawaka na yi. Waƙa daban, magana daban.

Maimakon haka, ka ɗauki makurofo ɗin kamar kunnen mutum, ka tabbatar da dangantaka mai ɗan nisa da shi.

Yana kuma da muhimmanci ka tabbatar da daidaicin sauti.

Tun da ba da wani cacirindon jama’a kake magana ba, babu dalilin yin ihu. Bai kuma kamata a ji ka kamar wani mai amfani da murya don tallar askirim shan manya ba, abin da shi ne ke aukuwa idan ka dinga yin raɗa a cikin makurofo.

Ka tuna da yin lumfashi

Idan ba ka yi lumfashi irin yadda ka saba ba za a ji ka a taurare.

Elspeth Morrison ta yi bayanin yadda, ta hanyar mancewa ka yi lumfashi, nan da nan mai zai ƙare maka, ka yi ta ƙoƙarin cika jawabinka da dakatawa inda bai kamata ba, abin da babu wanda zai so saurare.

Shi ya sa, domin taimaka maka ka lumfasa a wuraren da ya kamata, ka tabbatar ka yi alamu a kan abin da ka rubuta. Yi amfani da alamun tsayawa don yin lumfashi da kuma wataƙila, amfani da waƙafi don ƙara lumfasawa yadda za ka samu damar kaiwa ƙarshen jumla.

Kula da Muryarka

Kula da muryarka yadda ya kamata, ka kuma tabbatar ka gyatta ta kafin ka soma watsa shiri.

Mai horar da amfani da murya Elspeth Morrison ta bayyana cewa, a matsayinka na ɗan jaridar watsa labarai muryarka ce abin sana’arka.

Don haka tana buƙatar a kula da ita.

Game da abin da ke da amfani, ruwa shi ne babban abokin aikinka. Koyaushe ka tabbatar kana yawan shan ruwa a duka tsawon wunin da kake watsa shiri ko kuma kake ɗaukarsa.

Mine ne kuma bai da kyau?

Elspeth ta yi gargaɗin cewa a yi hattara da abubuwa irin su hayaƙi, da gahawa, da wasu abinci ko magunguna, waɗanda dukkansu suna iya busar da muryarka ko kuma su yi mata aibu ta wasu hanyoyin.

Abin da ya fi dacewa da murya ya sha bamban daga wannan mutum zuwa wancan, don haka shawara mafi kyawo ita ce ka ɗauki lokaci ka gano da kanka. Haka kuma, ka gano shi ma abin da bai dace da ita ba.

Shiryawa

Muryarka tana nuni ga yadda jikinka ke ji.

Dabarar ita ce a ji kada ƙarfinka a aikinka na dare ko na sassafe, ka yi kamar a farke kake sosai ko da ba hakan kake ji ba.

Akwai ‘yan dabarun da za ka iya amfani da su don sanyawa a ji muryarka a farke sosai tsawon wani gajeren lokaci.

Elspeth ta ba da shawar ka duba yadda ka zauna a gaban makurofo – zama a raggance zai sanya a ji murya ba kuzari a ciki. Shi ya sa wasu mutanen sun fi son tashi tsaye. Idan kana amfani da hannunka in kana magana ta yau da kullum, to ka yi hakan ma lokacin da kake watsa wani shiri – in ba haka ba, ba za a ji ka kamar yadda kake ba.