Ba da labarin wasanni

Mutane da dama suna daina saurare ne a duk lokacin da aka zo ba da labarin wasanni. Dalili shi ne, galibin mutane ba su damu da labarin wasannin ba. Sai dai akwai hanyoyin da za ka shawo kan masu saurarenka cewa labarin da za ka bayar ba na wasa ba ne kawai, in ji Ian Winter na nan BBC.

Ba da labarin wasanni

“Za ka yi mamakin cewa, wasu mutanen sukan tashi ne su tafi dafa shayi abinsu da sun ji an fara labarin wasanni.”

Wannan ba abin da ɗan jarida kamar Ian Winter na Today na BBC Midlands zai so ya ji ba ne.

Sai dai akwai hanyoyin da za ka shawo kan masu saurarenka cewa labarin da za ka bayar ba na wasa ba ne ‘kawai’ – hakan kuma yana da muhimmanci idan kana aiki ne a labaran komi da komi maimakon na wasanni kawai.

Ian ya nuna irin hanyar da za ka iya bi

  • Maida hankali a kan ɗan wasan maimakon wasan: labarin mutun da halin da yake ciki yana jan hankalin mutane, ko game da wasa ne ko wani abin daban.
  • Binciken wasa da kuma sana’o’in da ya haifar za su iya samar da labarai masu jan hankali kamar na kowane ɓangare na rayuwa.
  • Bi inda kuɗin suke: sau da yawa akwai labarai masu ban sha’awa da suka shafi masu kisan kuɗi da yawa, waɗanda ke saye ko saka jari a manyan wasanni.
  • Wake biya? Ba kowa ne daga cikin masu sauraren ka ba ke sha’awar wasanni...amma za su yi sha’awar jin a kan abin da ake kashe kudinsu – misali, filaye ko kayan wasannin da babu mai amfani da su
  • Yi amfani da bayanai game da mutane: ‘yan wasa maza da mata suna da su, ko sun shahara ko kuma ba su shahara ba sosai.
  • Bi hanyar amfani da kanka: idan hanyar da kake bi game shi wasan ne, yi kokarin nuna yadda kai kake ganin wasan.